2027: Dalilai 4 da Ke Iya Sa Tinubu Ya Rike Kashim Shettima a matsayin Mataimaki
- Duk da rade-radin sauya mataimaki, Bola Tinubu na iya cigaba da rike Kashim Shettima a 2027 saboda biyayya, daidaito da tasirinsa
- Shettima ya kasance amintaccen mataimaki ga Tinubu, yana tallata nasarorin gwamnatinsa da cigabanta tun a 2023
- Masana kamar Hakeem Baba-Ahmed sun ja kunnen Tinubu cewa cire Shettima zai iya jawo koma baya daga Musulmai a Arewa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ana yawan rade-radin cewa za a sauya Kashim Shettima daga takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027 a jam’iyyar APC mai mulki.
Rade-radin ya kara karfi bayan a taron masu ruwa da tsaki a Gombe na jam’iyyar APC ta amince da Tinubu a matsayin dan takara, ba tare da ambaton Shettima a cikin goyon bayan ba.

Source: Twitter
Zargin yunkurin sauya Shettima a matsayin mataimaki
Wani rahoton Punch ya ce za a yanke shawara ne kan matsayar kujerar Shettima bayan taron jam’iyyar APC na 2026.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa akwai yunkuri a jam'iyyar APC da ka iya sa a sauya Shettima, amma hadimin Tinubu, Bayo Onanuga ya bayyana cewa Tinubu bai dauki mataki ba tukuna.
Legit Hausa ta duba wasu dalilai da ka iya sa a sauya Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu:
1. Biyayyar Shettima ga Tinubu tun tuni
Kashim Shettima ya kasance tare da gwamnatin Bola Tinubu, yana bayyana nasarorin gwamnati kuma yana goyon bayan manufofinta.
Duk da ƙalubale iri-iri, ya ci gaba da kasancewa ginshiki mai ƙarfi, yana yawan yabon ubangidansa da kuma yada "nasarorin" wannan gwamnati.
Ana ganin Shettima a matsayin mai amana duba da irin jajircewa da yake yi wuri tabbatar da dorewar gwamnati tare da hakuri da zarge-zargen da ake yi cewa ba a ba shi dama a cikinta.
2. Addini da kuma lissafin siyasa
Kashim Shettima shi ma ya kasance Musulmi kamar Tinubu, yadda suka yi nasara a zaben 202 ana sa ran za su kuma a zaben da ke tafe na 2027.

Kara karanta wannan
'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai
Masu fashin baki da dama sun gargadi Tinubu kan ajiye Kashim duba da tasirin da zai iya yi a zaben da ke tafe.
Tsohon hadimin Tinubu, Hakeem Baba-Ahmed ya gargadi shugaban kan watsi da Arewacin kasar inda ya ce tsohon mai gidansa na bukatar kuri'u daga yankin, cewar Daily Post.
Baba-Ahmed ya ce Tinubu ya samu nasara ne dalilin tikitin Musulmi da Musulmi saboda haka bai kamata ya juya baya ga Musulman Arewa ba.
An ji malamai irinsu Sheikh Sani Yahaya Jingir suna cewa za su yi watsi da APC idan dai Bola Tinubu ya cire Kashim Shettima daga tikiti a 2023.

Source: Getty Images
3. Karfin siyasar Shettima a Arewa maso Gabas
Kashim Shettima ɗan asalin jihar Borno ne, jihar da ke yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.
Tasirinsa a yankin yana da girma, duba da rawar da ya taka a matsayin Gwamnan Borno daga 2011 zuwa 2019, da kuma matsayin da yake rike da shi yanzu na mataimakin shugaban kasa.
A lokacin da yake gwamna, ya jagoranci jihar da Boko Haram ta fi daɗewa tana addaba, inda ya samu yabo saboda ƙoƙarinsa wajen sake gina yankunan da rikici ya daidaita da kuma farfaɗo da rayuwar al'umma.
Matsayinsa na yanzu a matsayin mataimakin shugaban kasa ya ba shi damar magana kan matsalolin yankinsa da kuma tasiri wajen yanke manufofin da suka shafi yankin.
4. Barazanar Gwamna Zulum a Gombe
Tun farkon watan Yuni, shugabannin yankin Arewa maso Gabas na jam’iyyar APC sun gudanar da taro a Gombe, inda aka samu hatsaniya wurin mara wa Tinubu baya domin sake tsayawa takara a 2027.
An samu matsalar saboda ana zargin wasu na kiran sunan Tinubu ba tare da Shettima da hakan ya sanya shakku ko za a bar mataimakin shugaban a baya, cewar TheCable.
Gwamna Babagaba Zulum ya fusata da lamarin a matsayin yaron Shettima inda har yake cewa idan babu Kashim to babu APC a Arewa maso Gabas.
Hakan ya sa wasu masana ke ganin maganar za ta yi tasiri a zaben 2027 idan har aka saba duba da tasirin jam'iyyar a wasu jihohin yankin.
Shi ma Tinubu sai da ya fito yana babatu a Ogun kafin ya kai ga samun takara a zaben 2023.

Source: Facebook
Dalilai da ka iya sa Tinubu ya jefar da Kashim
A wani labarin mai kama da wannan, kun ji cewa ana rade-radin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai sauya mataimakinsa, Kashim Shettima kafin zaɓen 2027.
An yi ta yada hakan ne saboda matsin lamba daga wasu a Arewa ta Tsakiya da Kiristoci da ke neman a ba su kujera ta mataimaki, su na cewa an dade ana muzguna musu.
Wannan rahoto ya yi duba kan wasu dalilai da zai iya sa Bola Tinubu ya sauya Kashim a matsayin mataimakinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


