APC Ta Yi Martani Mai Zafi bayan Atiku, El Rufa'i da Peter Obi Sun Yi Hadaka a ADC

APC Ta Yi Martani Mai Zafi bayan Atiku, El Rufa'i da Peter Obi Sun Yi Hadaka a ADC

  • Jam’iyyar APC ta ce Bola Tinubu zai sake lashe zabe a 2027 duk da haɗewar manyan jam’iyyun adawa da ake ƙullawa
  • David Mark da Sule Lamido sun soki gwamnatin APC, suna cewa ta jefa ƙasa cikin halin kunci da rashin tsaro
  • Sai dai Bala Ibrahim na APC ya musu martani da cewa ƙoƙarin ƙulla kawancen 'yan adawa ba zai je ko ina ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da wasu fitattun ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa ke ƙara haɗa kai don kifar da Bola Ahmed Tinubu a 2027, jam’iyyar APC mai mulki ta ce hakan ba zai yi tasiri ba.

Jigo a jam’iyyar APC kuma mai magana da yawunta, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa kawancen da aka fara ƙulla wa a Abuja ba inda zai je.

Kara karanta wannan

2027: Sakataren hadakar ADC ya yi wa 'yan Najeriya bayanin fara aiki

Atiku da sauran 'yan adawa a taron hadin kai a Abuja
Atiku da sauran 'yan adawa a taron hadin kai a Abuja. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wasu daga cikin shugabannin kawancen sun amince su yi amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa don fuskantar APC a 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta yi wa David Mark da Sule martani

Tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, sun yi kaca-kaca da gwamnatin Tinubu a wata sanarwa da suka fitar bayan taronsu a Abuja.

Sanarwar, wadda David Mark ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa gwamnatin APC ce mafi muni da Najeriya ta taɓa samu, kuma lokaci ya yi da za a fatattake ta daga mulki.

Sannan sun yi kira ga ‘yan Najeriya su marawa sabon kawancen baya, domin ceto ƙasar daga halin matsin da ake ciki na tattalin arziki da tsaro.

Sai dai jam'iyyar APC ta ce sam babu kamshin gaskiya a cikin maganganunsu, domin a cewar Bala Ibrahim, Bola Tinubu ya taka rawar gani.

APC ta ce masu hadaka a ADC ba za su iya kifar da Tinubu ba.
APC ta ce masu hadaka a ADC ba za su iya kifar da Tinubu ba. Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Martanin APC kan hadakar su Atiku a ADC

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya ragargaji Atiku da sauran masu hadaka a 2027

Mai magana da yawun APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa duk wani yunƙurin kifar da Tinubu zai ci tura, inda ya ce jam’iyyar tana da karfi da shiri na sake lashe zabe.

Bala Ibrahim ya ce:

“Wannan kawance ba zai je ko ina ba, domin APC ta riga ta kafu a ƙasa kuma tana da goyon bayan jama’a.”

Duk da sukar da jam’iyyar ke fuskanta a fannoni daban-daban, APC na ganin cewa za ta sake samun nasara a 2027, yayin da jam’iyyun adawa ke fama da rikice-rikicen cikin gida.

APC ta soki masu hadaka a zaben 2027

A wani labarin, mun kawo muku cewa sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Ali Bukar Dalori ya ce suna shirye domin fuskantar masu kokarin hadaka a zaben 2027.

Ali Bukar Dalori ya bayyana cewa har yanzu jam'iyyar APC na nan da karfinta kuma babu wani shirin hadaka da zai girgiza ta a fadin Najeriya.

Sabon shugaban jam'iyyar ya ce zai mayar da hankali wajen samar da hadin kai a APC da warware dukkan wani sabani da 'ya'yan jam'iyyar suka samu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng