"Ba Dan Allah ba ne," An Gano Abin da Ke Tilastawa Gwamnonin PDP Sauya Sheƙa zuwa APC
- Kola Ologbondiyan ya yi zargin cewa gwamnonin PDP da ake ganin suna komawa APC tilasta masu aka yi amma ba haka suka so ba
- Tsohon kakakin PDP na ƙasa ya yi ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na danne gwamnonin ta yadda dole su yanke komawa APC
- Ya ce sulhun da Shugaba Tinubu ya yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike da Simi Fubara ba ƙaramar illa bace ga jam'iyyar PDP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon kakakin PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya yi zargin cewa gwamnonin PDP na komawa APC bisa tilas amma ba haka ransu ke so ba.
Ologbondiyan ya bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da surutu kan ganawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Tinubu ya gana da Fubara da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin Ribas: Sulhun Tinubu ya tayar da ƙura
A watan Maris, lokacin da rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike ya kai ƙololuwa, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a a jihar Rivers.
Ya kuma dakatar da gwamnan da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da kuma duka ƴan Majalisar dokokin jihar.
Sai dai a ranar Lahadi, shugaban ƙasa ya jagoranci zaman sulhunta Wike da Fubara, kuma daga bisani aka ga su suna murmushi tare da ɗaukar hoton hadin kai.
A halin yanzu kuwa, gwamnoni biyu na PDP, Sheriff Oborevwori na Jihar Delta da Umo Eno na Jihar Akwa Ibom, sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Dalilin da gwamnonin PDP ke komawa APC
Da yake magana a shirin Sunrise Daily na Channels tv a ranar Talata, Ologbondiyan ya ƙaryata ra’ayin cewa rikicin PDP ke janyo ficewar gwamnoni zuwa APC.
A cewarsa, ana danne haƙƙoƙin gwamnoni da aka zaɓa a PDP, domin tilasta musu shiga jam’iyyar mai mulki gabanin zaɓen 2027.
Ya ƙara cewa tsoma bakin Shugaba Tinubu wajen sasanta rikicin tsakanin Wike da Fubara wata babbar illa ce ga jam'iyyar PDP.

Source: Twitter
Ana zargin APC na tilastawa gwamnonin PDP
“Idan muka kalli abin da ke faruwa a jihar Ribas, zan faɗi gaskiya, ina ganin PDP ta yi iya bakin ƙoƙarinta, wasu ta hanyar da ba ta dace ba, wasu kuma da kyakkyawan niyya.
"Abin da PDP za ta fahimta daga wannan lamari shi ne cewa ana cin zarafin gwamnoninta.”
“Ana muzanta su, kuma ko da kuwa ba za su iya faɗa a fili ba, ana tilasta musu su bar jam’iyyarsu su koma APC tare da haɗewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.”
- Kola Ologbondiyan.
A ƙarshe, Ologbondiyan ya bukaci PDP da ta manta da abin da ya faru a Ribas, ta maida hankali wajen kare gwamnoninta, domin su guji duk wata barazana da ka iya kai su ficewa daga jam’iyyar.
Jagororin PDP a Kudu sun yi barazana
A wani labarin, mun kawo maku cewa Gwamna Peter Mbah ya gargaɗi PDP cewa Kudu maso Gabas za ta sake nazari kan ci gaba da zama a jam'iyyar adawa.
Hakan dai na cikin abubuwam da masu ruwa da tsakin PDP a yankin suka tattauna a taron da suka gudanar a jihar Enugu.
Da yake zantawa da ƴan jarida bayan taron, Gwamna Mbah na Enugu ya yi barazanar cewa yankin na iya ficewa daga jam’iyyar PDP.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


