2027: APC Ta Fadi Yadda Jihar Sakkwato kadai Ta Isa Kai Tinubu ga Nasara a Arewa
- Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Isa Sadiq-Achida, ya bayyana yan siyasar da ke cikin hadakar adawa da cewa ba su da katabus
- Ya ce dukkaninsu na da matsala da mutanensu, saboda haka ba a tsammanin za su yi wani tasiri a kan sakamakon zaben 2027 da ke zuwa
- Alhaji Achida, ya kara da cewa ko da an yi nasarar kulla hadakar, jihar Sakkwato kadai ta isa taimaka wa APC da abin da ta ke bukata
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sakkwato – Shugaban jam’iyyar APC a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Sadiq-Achida, ya ce kokarin kafa hadakar siyasa a Arewacin Najeriya ba za ta iya tabuka komai ba zabe mai zuwa.
Ya ce dukkanin wadanda ke cikin hadakar na fama da matsalolin cikin gida, yayin da sauran kuma suka rasa farin jini a tsakanin talakawa masu kada kuri'a.

Source: Facebook
A wata hira da ta kebanta da jaridar Punch, wacce aka yi a Fadar Gwamnati ta Jihar Sakkwato a ranar Asabar, Sadiq-Achida ya ce babu wanda zai hana Bola Ahmed Tinubu samun nasara a Arewa a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan adawar Arewa ba su da tasiri – APC
Sadiq-Achida ya bayyana cewa waɗanda ke kokarin kafa wannan hadaka a Arewa ba su da wani tasirin a zo a gani da zai iya shafar sakamakon zabe.
A cewarsa:
“Ko da wata hadaka ta fito a Arewa, Sakkwato kadai za ta iya bada kuri’un da za su cike gibin da kowace jiha ta gaza domin Bola Tinubu ya kai ga samun nasara."
Shugaban APC na Sakkwato ya kalubalanci tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana mai cewa ya raba gari da jama’ar jiharsa, musamman mutanen Kudancin Kaduna.
“Ban ganin El-Rufai na da wani tasiri a siyasance a Jihar Kaduna. Ya raunana mutanen Kudancin Kaduna kwarai da gaske a lokacin gwamnatinsa. Ko damarsu ta kada kuri’a bai bar su da ita ba.”

Kara karanta wannan
'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai
Jam'iyyar APC ta caccaki Atiku Abubakar
Achida ya yi tsokaci kan halin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ke ciki, yana cewa yana fama da rikice-rikice a cikin jam’iyyar PDP da kuma rashin karbuwa a Jihar Adamawa.

Source: Facebook
Ya ce:
“Kowa ya san cewa Sanata Aishatu Binani ce ta ci zabe a Adamawa, amma wani abu daban ya faru. Atiku har yanzu yana fama da Gwamnan jiharsa, har an kwace masa sarautar gargajiya kwanan nan. Wannan ya bayyana irin halin da yake ciki.”
Sadiq-Achida ya bayyana wadanda ke bayan wannan hadaka ta Arewa a matsayin mutane da ba su da karfi a kasa, yana mai cewa suna fafutuka ne ba tare da samun goyon bayan talakawa ba
Hadakar adawa ta shirya tunkarar APC
A baya, mun wallafa cewa kungiyar hadakar jam’iyyun adawa ta shirya fafutukar kwace kujerar shugaban kasa daga hannun Bola Ahmed Tinubu na APC a babban zaben 2027 mai zuwa.
Rahotanni sun ce ta shirya sanar da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasarta na gaba domin kalubalantar Shugaba Tinubu bisa ikirarin cewa ya gaza taimakon 'yan Najeriya.
Tun farko an yi niyya a kafa kawancen ne karkashin SDP, amma bayan dogon tattaunawa da rashin jituwa, mafi yawan shugabannin hadakar sun yanke shawarar komawa ADC.
Asali: Legit.ng

