Murabus ɗin Ganduje: An Bayyana Matakin Farko da Sabon Shugaban APC Ya Dauka

Murabus ɗin Ganduje: An Bayyana Matakin Farko da Sabon Shugaban APC Ya Dauka

  • APC ta karɓi murabus ɗin Abdullahi Ganduje daga muƙamin shugabancin jam'iyyar na ƙasa, inda Ali Bukar Dalori ya zama muƙaddashin shugaba
  • An bayyana cewa Ganduje ya yi murabus ne saboda rashin lafiya, amma wasu majiyoyi sun ce matsin lamba ne daga yankin Arewa ta Tsakiya
  • Dalori ya yi alƙawarin ƙarfafa jam'iyyar APC da inganta dimokraɗiyya a ciki, yana mai godiya ga Shugaba Bola Tinubu bisa jajircewarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin gudanarwar na kasa (NWC) na APC ya sanar da amincewa da murabus ɗin tsohon shugaban Jam'iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

An sanar da hakan ne yayin taron NWC na jam'iyyar karo na 174, wanda sabon muƙaddashin shugaban jam'iyyar na kasa, Ali Bukar Dalori, ya jagoranta.

Sabon shugaban APC ya gudanar da taron NWC na jam'iyyar karon farko bayan murabus din Ganduje
Muƙaddashin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori, yayin taron NWC na jam'iyyar karo na 174 a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Kwamitin ya nuna godiya ga jagorancin Ganduje tare da yi masa fatan samun sauƙin rashin lafiyarsa cikin gaggawa, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Murabus ɗin ya fi masa alheri': Jigon APC ya faɗi wulaƙanci da aka shiryawa Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu dalilai da suka tilastawa Ganduje murabus

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga muƙaminsa a ranar Juma’a, matakin da mutane da yawa basu zata ba.

A cikin takardar murabus ɗinsa, Ganduje ya bayyana cewa ya ajiye muƙamin ne saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, yana mai cewa yana so ya fi mai da hankali kan lafiyarsa yanzu.

Sai dai, wasu majiyoyi sun ce murabus ɗin nasa ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya, wanda hakan ya haifar da rikicin shugabanci a jam’iyyar.

Yayin da kuma wasu majiyoyi suka ce Shugaba Bola Tinubu ne ya umurce shi da murabus, bayan rahoton Hukumar Tsaron Jiha (DSS) da ya zarge shi da cin hanci da rashawa.

Majiyar ta ce abin da ya fi jawo matsin lamba shine yadda aka tafka magudi a zaɓen fitar da gwani na ƙaramar hukumar Bwari da ke Abuja, wanda har ya jawo wani ya mutu.

Kara karanta wannan

Ana zargin an taso na kusa da Tinubu ya yi murabus domin karɓar kujerar Ganduje

Dalori ya yi alkawari kan shugabancin APC

Yayin jagorantar taron NWC karo na 174, Ali Dalori ya tabbatar wa mambobin jam'iyyar da jama'a cewa APC za ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi da haɗin kai, inda ya ƙara da cewa:

"APC za ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya, kuma gida ga kowa."

Ya kuma yi alkawarin cewa zai yi aiki tare da sauran mambobin NWC don inganta dimokraɗiyyar cikin gida da ƙarfafa jam'iyyar.

Ali Bukar Dalori ya kuma gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa ga ci gaban jam'iyyar APC da kuma ƙasa baki ɗaya.

Mukaddashin APC din ya yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan shirin gwamnati na Renewed Hope, wanda ke mai da hankali kan haɓaka ci gaban tattalin arziki, zaman lafiya, da kwanciyar hankali a siyasar Najeriya.

Sabon shugaban APC, Ali Dalori ya sha alwashin dorewar hadin kai a jam'iyyar
Muƙaddashin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori, yayin taron NWC na jam'iyyar karo na 174 a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Ali Bukar Dalori ya shiga ofishin APC

'Yan majalisar NWC na APC sun nuna kwarin gwiwa ga tsarin miƙa mulki kuma sun yi alƙawarin goyon bayan Dalori da kuma babban burin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan hasashe da dama, an gano 'dalilin' murabus din Ganduje daga shugabancin APC

Wata sanarwa da Legit Hausa ta gani a shafin APC na X ya nuna cewa Ali Bukar Dalori, ya kama aiki a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam'iyyar.

Sanarwar ta ce:

"A yau Litinin, sabon muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Hon. Ali Bukar Dalori, ya kama aiki kuma a halin yanzu yana jagorantar taron kwamitin gudanarwa na ƙasa a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja."

Karanta sanarwar a kasa:

'Yan Borno sun jefo zargi bayan murabus ɗin Ganduje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan jihar Borno sun nuna rashin jin daɗinsu bayan murabus ɗin Abdullahi Ganduje daga kujerar shugabancin jam'iyyar APC.

Mafi yawan mazauna jihar sun bayyana cewa hakan wata dabara ce ta hana Kashim Shettima samun tikitin mataimakin shugaban ƙasa a 2027.

Sun bayyana cewa sauya shugabancin jam'iyyar APC daga Ganduje zuwa wani daga Borno zai iya kawo sauyi a tsarin yankin, wanda zai iya shafar damar Shettima ta siyasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com