'Babu Hadaka da Atiku,' Peter Obi Ya Ce zai Yi Takara a 2027, Zai Yi Wa'adi 1 Kawai
- Yayin da ake maganar 2027, Peter Obi ya ce zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar LP
- Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan na Anambra ya ce zai yi wa’adi guda kacal idan ya ci zabe a 2027
- Peter Obi ya bayyana abubuwan da za su zama masu muhimmanci a mulkinsa wanda su ne tsaro, ilimi da yaki da talauci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2027 mai zuwa.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye da magoya bayansa a daren Lahadi, inda ya ce idan Allah ya ba shi nasara, zai yi wa’adi daya kacal na shekaru hudu.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa a wani bayani da kakakinsa, Ibrahim Umar, ya fitar a ranar Litinin ya ce Obi bai da niyyar yin hadakar takara da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai duk da haka ya ce ya bude kofar tattaunawa da kowacce jam’iyya da ke da burin ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Abin da Obi zai yi cikin shekara 2 na farko
Obi ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar kawo daidaito a cikin kasa cikin shekaru biyu kacal da fara mulkinsa. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai da shi don ceto kasar.
Vanguard ta wallafa cewa ya ce:
“Ina da tabbacin zan kawo zaman lafiya da daidaito a Najeriya cikin shekara biyu,”
Ya kuma ce ba zai amince da wata kawance ba sai dai idan za ta fi mayar da hankali kan dakile kashe-kashe a jihohi kamar Benue da Zamfara, farfado da tattalin arziki, da samar da abinci.

Kara karanta wannan
'Murabus ɗin ya fi masa alheri': Jigon APC ya faɗi wulaƙanci da aka shiryawa Ganduje
Peter Obi ya caccaki tafiyar Tinubu St. Lucia
Peter Obi ya bayyana rashin jin dadinsa kan rahoton da ke cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara hutun kwana 10 a ƙasar St. Lucia. Ya ce hakan bai dace ba da halin da Najeriya ke ciki ba.
A cewarsa:
“Mutane na mutuwa a Benue da Borno, amma shugabanninmu suna bikin bude matattarar motocin haya ko kuma suna zuwa hutu ƙasashen waje,”
Manya alkawuran da Obi ya yi wa Najeriya
Obi ya bayyana cewa a cikin kwanaki 100 na farko da fara mulkinsa, zai maida hankali kan samar da tsaro, bunkasa ilimi da rage talauci.
Tsohon gwamnan ya ce kudin gwamnati za su tafi ne kai tsaye zuwa manyan fannonin raya kasa a mulkinsa.

Source: Twitter
Obi ya ce muddin ya zama shugaban kasa, ba za a sake samun sauya sheka daga jam’iyya zuwa wata jam’iyya ba. Ya ce zai dawo da tsarin siyasa mai karfi da ‘yanci ga ‘yan adawa.

Kara karanta wannan
Rubdugu kan 'yan adawa: An rusa kamfanin kanin Peter Obi bayan cire rawanin Atiku
Obi ya yaba wa Ganduje kan murabus
A wani rahoton, kun ji cewa Peter Obi ya yaba wa Abdullahi Umar Ganduje kan murabus da ya yi a makon da ya wuce.
Abdullahi Ganduje ya yi bayyana rashin lafiya a matsayin dalilin da ya sanya shi ajiye kujerar shugabancin APC.
Peter Obi ya ce akwai abin koyi a abin da Abdullahi Ganduje ya yi na ajiye mulki saboda ganin ba zai iya sauke nauyin aikinsa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
