Abba Kabir da Gwamnonin Adawa 4 da Jam'iyyar APC ke Son Jowowa kafin 2027

Abba Kabir da Gwamnonin Adawa 4 da Jam'iyyar APC ke Son Jowowa kafin 2027

  • APC mai mulki ta ce tana shirin jawo gwamnonin jihohi biyar zuwa jam’iyyar kafin babban zaben da za a shirya a shekarar 2027
  • An ambaci jihohin Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano da daya daga Abia ko Enugu a cikin jerin jihohin da APC ke shirin canzawa ra'ayi
  • A cewar jam'iyyar APC, hadakar 'yan adawa da Atiku Abubakar da Peter Obi ke kokarin ginawa a Najeriya ba za ta yi tasiri ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta bayyana sabon yunkurinta na janyo wasu gwamnonin adawa zuwa jam’iyyar kafin zaben 2027.

Wannan yunkurin na zuwa ne kasa da mako daya bayan murabus din Dr Abdullahi Ganduje, wanda hakan ya sake janyo ce-ce-ku-ce a cikin gungun ‘yan adawa.

APC na son jawo gwamnoni 5 kafin zaben 2027
APC na son jawo gwamnoni 5 kafin zaben 2027. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa daga Kudu maso Gabas, Dr Ijeoma Arodiogbu ne ya bayyana hakan cikin wata hira da Punch.

Kara karanta wannan

Bayan Ganduje, APC ta budewa Kwankwaso kofar sauya sheka da aiki da Bola Tinubu

Gwamnonin jihohi 5 da APC ke kokarin jowowa

Dr Arodigbu ya ce shirin bai tsaya a kan hasashe ba kawai, domin kuwa zuwan gwamnonin APC abu ne da ya kusa tabbata.

Arodiogbu ya ce:

“Jihohin da muke magana a kai sun hada da Bayelsa, Rivers, Plateau, Kano da daya daga cikin Abia ko Enugu.
"A cikin watanni biyu masu zuwa, za ku ga su a hukumance sun shiga APC.”

Ya kara da cewa, sauya sheka da Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, da Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori suka yi tare da wasu tsofaffin gwamnoni da ‘yan majalisa, alama ce ta raunin adawa.

Haka kuma, Gwamnan Anambra, Charles Soludo na jam’iyyar APGA, ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu a karo na biyu, kodayake APC ta musanta cewa an cimma wata yarjejeniya da shi.

APC ta ce hadakar Atiku ba za ta yi tasiri ba

Rahotanni sun ce Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP na kokarin kafa hadakar adawa don fuskantar APC a 2027, amma Arodiogbu ya ce hakan ba zai yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Ganduje: Jerin shugabannin APC da yadda suka sauka daga shugabanci

A cewarsa:

“Ina kallon wannan hadakar adawa a matsayin dabarar jan hankali ne kawai. ‘Yan Najeriya na goyon bayan jam’iyya da ke kawo ci gaba, wato APC,”

Ya ce ana cigaba da tattaunawa da gwamnonin jihohi da dama a fadin kasar, ciki har da yankunan da galibin adawa ke da karfi kamar Kudu maso Gabas.

APC ta yi yarjejeniya da gwamna Soludo?

Arodiogbu ya musanta cewa an cimma wata yarjejeniya da Gwamna Charles Soludo domin samun goyon bayan APC a 2027, yana mai cewa shugaban kasa bai amince da hakan ba.

Ya bayyana cewa:

“A lokacin da Shugaba Tinubu ya kai ziyara Anambra domin bude cibiyar Emeka Anyaoku, mun gabatar masa da dan takararmu, Nicholas Ukachukwu. Ya ce mu je mu nemi nasara, ba ya tare da Soludo,”

Ya kara da cewa:

“Soludo ba shi da farin jini yanzu. Ya shafe shekaru biyu yana sabani da sarakunan gargajiya, limaman coci da kungiyoyin ‘yan kasuwa.”

Kara karanta wannan

'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo. Hoto: Anambra State Government
Source: Twitter

Legit ta tattauna da Musa Idris

Yayin zantawa da wani dan jihar Kano, Musa Idris ya bayyana ra'ayinsa kan yiwuwar komawar Abba Kabir Yusuf APC.

A cewar Musa:

"Idan zai cigaba da ayyukan da yake masu kyau, ko ya koma APC ba zai rasa magoya baya ba. Amma ni kam da wahala na goyi bayansa a APC."

Gwamnonin APC sun yi taro a Edo

A Wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar APC 23 sun yi wani taro na kwana biyu a jihar Edo.

Hakan na zuwa ne 'yan sa'o''i bayan murabus din da tsohon shugaban jam'iyyar, Abdullahi Ganduje ya yi.

Gwamnonin sun bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan hadin kai da kawo cigaba a dukkan jihohin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng