2027: Matasan APC Sun Bullo da Dabarar Rakitowa Tinubu Kuri'a Miliyan 10

2027: Matasan APC Sun Bullo da Dabarar Rakitowa Tinubu Kuri'a Miliyan 10

  • Shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel ya ce sun bullo da hanyar kara sama wa shugaban kasa, Bola Tinubu kuri'a a zaben 2027
  • Ya ce a yanzu haka, an kammala shirin bude sabuwar cibiyar matasa da za ta tattaro kawunan matasan Najeriya don cimma muradin Tinubu
  • Haka kuma fatan cibiyar za ta taimaka wajen nuna wa matasan muhimmancin Tinubu, da amfanin sake zazzaga masa kuri'a a zaben gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa, Dr. Dayo Israel, ya bayyana cewa sashen matasan jam’iyyar na shirin bude sabuwar cibiyar cibiyar ci gaban matasa.

An tsara cibiyar ne domin hada kan matasa da ayyuka daban-daban da suka shafi burin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gina Najeriya mai inganci.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun yiwa PDP barazana ana fama da rikicin cikin gida

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Matasan APC sun fara fafutukar zaben 2027 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dr. Israel da ya bayyana hakan a shafinsa na X, ya ce cibiyar za ta kunshi ofishin shugaban matasan APC na kasa, da kuma ofishin gudanarwa na sashen matasa na jam’iyyar, a unguwar Wuse 2 a Abuja.

Za a tarkatowa Tinubu matasa

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Dayo Israel ya kuduri aniyar jawo hankalin karin matasa su shiga jam’iyyar APC, tare da kokarin samar da kuri’u miliyan 10 ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Ya ce cibiyar za ta kasance wani muhimmin mataki na dabarun janyo matasa da kuma karfafa goyon baya ga sake zaben Tinubu a shekarar 2027.

Dr. Israel ya ce nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Tinubu ke samu a tsakanin matasa ne suka ba shi kwarin guiwa da sha’awar wannan aiki.

Ana son a sake zaben Tinubu
Matasan APC sun yiwa Tinubu alkawarin kuri'a miliyan 10 Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daga cikin shirye-shiryen da ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar domin matasa akwai tsarin lamunin dalibai da kuma shirin P-CNGi.

Ya ce wadannan ayyuka na daga cikin matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta dauka wajen inganta rayuwar matasa, saboda haka suke son a ramawa kura aniyarta.

Kara karanta wannan

'Ganduje ya jawo wa Kano abin kunya,' NNPP ta yi magana kan komawar Kwankwaso APC

Ana son a sake zaben Tinubu

Kungiyar matasan APC ta bayyana cewa dole ne a sake zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu idan ana so ya kammala ayyukan alheri da ya fara a wa’adin farko.

Dayo Israel ya ce:

"Tun lokacin da na tsaya takarar shugaban matasa na kasa, na kuduri aniyar kafa wannan cibiya. Hakan ya kasance cikin kudirina, amma babu wanda ya yarda da ni ko ya tallafa. Sun kasa ganin abin da na gani."

Ya kara da cewa:

"Babban burinmu shi ne mu shiga zukatan matasan Najeriya ta hanyar sake fasalin yadda suke kallon APC da kuma kara yawan 'yan jam'iyya matasa."

Israel na ganin da zarar komai ya dauki harama, za a iya jawo matasan Najeriya zuwa tafiyar Bola Tinubu idan ya ayyana aniyar sake tsayawa takara a shekarar 2027 mai zuwa.

Dattawan Arewa sun roki Tinubu alfarma

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar NEF ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya gaggauta daukar matakin ayyana dokar ta-ɓaci a yankin Arewacin Najeriya saboda tabarbarewar tsaro.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da maganar Ganduje, an yaɗa murabus ɗin sakataren gwamnati, gaskiya ta fito

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abubakar Jiddere, mai magana da yawun kungiyar, ya fitar, inda ya bayyana cewa lamarin ya kai wani mataki da ba za a iya yin shiru ba.

Kungiyar ta ce yankin Arewa na fama da tashe-tashen hankula a Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma, da Arewa maso Gabas, inda jama’a ke rasa rayuka da dukiyoyi a kullum, kuma babu alamun sassauci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng