'Ganduje Ya Jawo wa Kano Abin Kunya,' NNPP Ta Yi Magana kan Komawar Kwankwaso APC

'Ganduje Ya Jawo wa Kano Abin Kunya,' NNPP Ta Yi Magana kan Komawar Kwankwaso APC

  • Magoya bayan Rabiu Kwankwaso sun bayyana cewa tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jawo wa jihar Kano abin kunya
  • Shugaban jam'iyyar na Kano, Hashimu Dungurawa da ya bayyana haka, ya ce ana zargin Ganduje da karbar na goro a zaben APC a Abuja
  • Dungurawa ya ce an samu rahoton bayan Ganduje ya karbi kudi daga hannun wasu 'yan APC ne aka tilasta masa rabuwa da shugabancin jam'iyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Masu goyon bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirye-shiryen daukar mataki na gaba dangane da jam’iyyar APC.

Wannan na zuwa ne bayan murabus da tsohon abokin tafiyar Kwankwaso kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Umar Abdullahi Ganduje ya yi daga kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Kara karanta wannan

Abba Kabir da gwamnonin adawa 4 da jam'iyyar APC ke son jowowa kafin 2027

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
NNPP ta ce Kwankwaso ne kawai zai iya magana kan sauya shekarsa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A labarin da ya kebanta ga Jaridar Leadership, ta ruwaito cewa tun bayan hawansa mulki, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Kwankwaso don tattauna yiwuwar komawarsa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai abokan tafiyarsa na ganin cewa Kwankwaso ba zai iya shiga APC ba yayin da Ganduje ke matsayin shugaban jam’iyyar.

‘Yan kwankwasiyya sun sako Ganduje a gaba

Wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya, sun bayyana cewa Ganduje ya batawa al’ummar Kano suna, kuma hakan ne ya sa aka tilasta masa ya sauka daga mukaminsa.

Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin abin kunya ga Kano.

Ya ce an samu Ganduje da laifin cin hanci da rashawa, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyya da aka kammala kwanan nan.

Hashimu Dungurawa
Shugaban NNPP ya zargi Ganduje da jawo wa Kano abin kunya Hoto: Mustapha Kakisu Yalwa
Source: Facebook

Dungurawa ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa an tilastawa Ganduje yin murabus ne saboda cin hanci da rashawa da aka tabbatar yana aikatawa

Kara karanta wannan

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun yiwa PDP barazana ana fama da rikicin cikin gida

Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC?

Sai dai Dungurawa ya ce ba zai iya tabbatar da ko murabus da Ganduje ya yi zai sa jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya koma jam’iyyar APC ba.

A cewarsa:

“Ba zan iya yanke hukunci ko magana a kan ko jagoran Kwankwasiyya zai koma jam’iyyar APC mai mulki ba."
"Game da Ganduje kuwa, an umarce shi da ya yi murabus. Akwai zarge-zargen cin hanci da rashawa a kansa."
"Na karanta a jaridu cewa ya aikata rashawa a zaben shugabannin jam’iyya a majalisun kananan hukumomi a Abuja. An kama shi da sauya wakilai da karbar cin hanci.”

NNPP: 'Ba laifi don Kwankwaso ya koma APC'

A baya, mun wallafa cewa NNPP ta ce ba ta damu ba da rade-radin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC, har ma ta bayyana hakan a matsayin abin farin ciki.

Wannan na zuwa ne bayan murabus da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi, da kuma rade-radin cewa tsohon gwamnan Kano, Kwankwaso zai sauya sheka.

NNPP ta bayyana matsayarta ne ta cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Legas, inda ya ce za su yi maraba da matakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng