'Abin Murna Ne': NNPP Ta Faɗi Matsayarta kan Rade Radin Kwankwaso Zai Koma APC

'Abin Murna Ne': NNPP Ta Faɗi Matsayarta kan Rade Radin Kwankwaso Zai Koma APC

  • Jam’iyyar NNPP ta bayyana matsayarta kan jita-jitar cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai bar cikinta
  • NNPP ta za ta ji dadi da kwanciyar hankali idan Kwankwaso ya bar jam’iyyar ya koma APC, bayan rikicin cikin gida
  • Sakataren NNPP ya ce Kwankwaso ya kawo musu matsala da rikicin tambari da kararraki, duk da cewa an kore shi daga jam’iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja , Lagos- Jam’iyyar NNPP ta yi martani kan rade-radin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC.

Jam'iyyar ta ce za ta samu saukin rai idan dan takararta na 2023, Kwankwaso, ya bar cikinta zuwa APC.

NNPP ta yi magana kan rade-radin Kwankwaso zai koma APC
NNPP ta ce abin farin ciki ne Kwankwaso zai koma APC. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

NNPP ta magantu bayan murabus din Ganduje

Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na kasa, Mista Oginni Olaposi, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Legas, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

'Murabus ɗin ya fi masa alheri': Jigon APC ya faɗi wulaƙanci da aka shiryawa Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olaposi ya yi wannan bayani ne a martani kan murabus din shugaban APC, Abdullahi Ganduje, da rade-radin cewa Kwankwaso zai koma APC.

Ganduje ya sauka daga mukaminsa na shugabancin jam’iyyar APC a ranar Juma’a, yana mai cewa dalilan lafiyarsa ne suka sa ya ajiye.

Jam'iyyar NNPP ta caccaki halayen Sanata Kwankwaso

Olaposi ya ce ko da yake wannan lamari na cikin APC ne, NNPP ta ga dacewar magana saboda rikicin tsakaninta da Kwankwaso.

Ya ce:

“Kwankwaso har yanzu yana dagewa cewa mamban jam’iyyarmu ne duk da cewa mun kore shi saboda ayyukan sabawa jam’iyya.
“Kwankwaso bai tsaya nan ba, ya yi kokarin kwace jam’iyyar NNPP tare da jefa ta cikin shari’o’in da za a iya kaucewa.
“Tambarin NNPP da ya mayar da na Kwankwasiya, yanzu INEC ta dawo da na NNPP bayan shekaru na rikici da shari’a.
“Muna da dalilin da zai sa mu yi shakku da jita-jitar cewa Ganduje ya bar APC don wata yarjejeniya da Kwankwaso kafin 2027.

Kara karanta wannan

Ana zargin an taso na kusa da Tinubu ya yi murabus domin karɓar kujerar Ganduje

“An taba cewa Ganduje ya fadi cewa APC koyaushe a shirye take ta yafe wa wadanda suka sauya sheka daga cikinta."
NNPP ta fadi matsayarta kan barin Kwankwaso jam'iyyar
NNPP ta ce za ta yi murna idan Kwankwaso ya bar APC. Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

Abin da NNPP za ta yi bayan fitar Kwankwaso

Olaposi ya ce NNPP za ta yi murna idan Kwankwaso ya koma APC, saboda jam’iyyar na da karfin daukar nauyin matsalolinsa, cewar rahoton Punch.

“Abu ne mai wahala mu gaskata cewa Kwankwaso, wanda har yanzu ke kokarin kwace NNPP, yana shirin komawa APC.
“Kwankwaso ya yaudare mu, ya nemi kwace jam’iyyar daga hannun wanda ya kafa ta, Dr. Boniface Aniebonam."

- Cewar Olaposi.

Kano: NNPP ta gargadi alakanta Kwankwaso da APC

Kun ji cewa shugabannin bangarori biyu na NNPP a Kano sun yi magana kan rade-radin cewa ana son ba Rabiu Kwankwaso muƙamin mataimakin shugaban kasa.

Shugabannin sun gargadi jama’a ka da su jawo sunan Kwankwaso cikin batun mataimakin Bola Tinubu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Sun bayyana cewa Kwankwaso bai da niyyar shiga APC, kuma kiraye-kirayen da ake yi masa bisa cancanta ne ba wai shiri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.