'Murabus din Ganduje Ya Bude wa Kwankwaso Kofar Shiga APC,' Jigon Jam'iyya
- Wani jigo a jam’iyyar APC ya yi hasashen cewa murabus din Abdullahi Ganduje na iya bude kofar shigar Rabiu Kwankwaso jam’iyyar
- Ya ce dama Abbdullahi Ganduje na rike ne da kujera ce da aka ware wa yankin Arewa ta Tsakiya, kuma hakan ya yi kokarin kawo rikici
- Jigon ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso ya karɓi shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa idan har ya sauya sheka zuwa cikinta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan murabus din Abdullahi Umar Ganduje daga shugabancin APC, wani jigo a jam’iyyar ya ce hakan na iya bude hanya ga Rabiu Musa Kwankwaso.
Jigon, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa ko da yake Ganduje ya rike kujerar tun daga watan Agustan 2023, yankin Arewa ta Tsakiya ne ya kamata ya rike mukamin.

Source: Twitter
A hirar da the Guardian ta yi da jigon, ya ce kasancewar murabus din Ganduje ya zo a ba zata, zai iya jefa rudani a APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ya sa Abdullahi Ganduje ya yi murabus?
Tun bayan fitowar labarin murabus din Abdullahi Ganduje daga kujerar APC mafi girma, mutane suka fara maganganu kan dalilin hakan.
Sai dai kusa a jam'iyyar ya ce:
"Wata kila an tilasta Ganduje ya yi murabus ne, domin ba kasafai ake ganin shugaban APC ya gama wa’adinsa ba. Mun gani a kan Abdullahi Adamu, Oshiomhole da wasu da suka gabata."
Ya kara da cewa rikicin rabon mukamai na iya haddasa murabus din Ganduje daga shugabancin jam’iyyar.
A cewarsa:
"Ya kamata kujerar shugaban jam’iyyar ya kasance a yankin Arewa ta Tsakiya ne tun farko. Amma an bai wa Ganduje daga Arewa maso Yamma."
Kwankwaso zai iya maye gurbin Ganduje?
A ƙarshe, jigon ya bayyana ra’ayinsa na cewa Sanata Kwankwaso na iya zama shugaban jam’iyyar APC mai zuwa.
Ya bayyana cewa:
"Daga yadda abubuwa ke tafiya, ina ganin Kwankwaso zai dawo APC kuma zai iya zama shugaban jam’iyyar,"
Alakar murabus din Ganduje da rikicin Gombe
Da aka tambaye shi ko akwai alaka tsakanin murabus ɗin Ganduje da rade-radin sabani tsakaninsa da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, jigon ya musanta hakan.
A cewarsa:
"Abin da ya faru a taron APC na Arewa maso Gabas a Gombe wani salo ne da Shugaba Tinubu ya shirya domin gano karfin APC a yankin. Bai da alaka da cire Shettima ko Ganduje."

Source: Twitter
Ficewar Ganduje za ta shafi APC a Kano?
Jigon ya ce ba lallai ficewar Ganduje ta shafi APC a Kano ba, yana mai bayyana Ganduje a matsayin mamba mai biyayya da ƙwazo.
A cewar shi:
"Ban ga dalilin da zai sa Ganduje ya yi adawa da Shugaba Tinubu ba. Yana da biyayya kuma yana da sadaukarwa a jam’iyyar APC,"
APC ta yarda da murabus din Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta tabbatar da murabus din shugabanta, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Felix Morka ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.
Felix Morka ya ce APC ta yaba da kokarin da Abdullahi Ganduje ya yi a lokacin shi, kuma tana mi shi fatan alheri a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


