Ana tsaka da Batun Murabus ɗin Ganduje a APC, Kwankwaso Ya Buɗe Sabon Ofis a Abuja

Ana tsaka da Batun Murabus ɗin Ganduje a APC, Kwankwaso Ya Buɗe Sabon Ofis a Abuja

  • Ɗan takarar NNPP a zaben shugaban ƙasar 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da sabon ofishin jam'iyya reshen Abuja yau Juma'a
  • Hadimin Kwankwaso ya ce shugabannin NNPP da masu ruwa da tsaki da ɗumbin magoya baya sun halarci wurin buɗe ofishin a Wuse Zone 6
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da labarin murabus din shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya karaɗe kafafen sada zumunta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da labarin murabus ɗin shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya karaɗe Najeriya, an hangi jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a Abuja.

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da sabon ofishin jam'iyyar NNPP a babban birnin tarayya Abuja yau Juma'a, 27 ga Yuni.

Kara karanta wannan

An gano yadda aka tilastawa Ganduje yin murabus daga shugabancin APC

Jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Kwankwaso.
Kwankwaso ya kaddamar da sabon ofishin NNPP a Abuja Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Mai taimakawa Kwankwaso kan harkokin yada labarai, Hon. Saifullahi Hassan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya buɗe sabon ofishin NNPP

Sanarwar ta ce jagoran NNPP ya kaddamar da babban ofishin jam'iyyar reshen Abuja a unguwar Wuse Zone 6.

Taron ya samu halartar manyan ƙusoshin jam'iyyar ciki har da shugaban NNPP na ƙasa, Dr. Ahmed Ajuji da sauran ƴan kwamitin gudarwa (NWC) da ɗimbin magoya baya.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan rahotanni sun karaɗe kafafen watsa labarai cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC.

Ana raɗe-raɗin Tinubu zai jawo Kwankwaso

Wasu dai na ganin wannan murbaus ba zato ba tsammani ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na jawo Kwankwaso zuwa cikin APC ba.

Kwankwaso dai shi ne babban abokin hamayyar Ganduje a jihar Kano kuma an daɗe ana alaƙanta jagoran NNPP da komawa APC domin aiki a gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC 23 sun gana da juna bayan murabus din Ganduje

Sai dai ana cikin wannan raɗe-radi ne aka ga Kwankwaso ya buɗe sabon ofishin NNPP reshen Abuja.

Kwankwaso a sabon ofishin NNPP.
Kwankwaso ya halarci taron bude ofishin NNPP a Abuja Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Shugabannin NNPP sun halarci taron a Abuja

"Jagoran NNPP na ƙasa, Mai Girma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, (PhD, FNSE) a yau Jumma’a, 27 ga Yuni, 2025, ya kaddamar da sabon ofishin jam’iyyar NNPP reshen Abuja da ke Wuse Zone 6, Abuja.
"Taron ya samu halartar Shugaban jam’iyya na ƙasa, Dr. Ahmed Ajuji, tare da wasu fitattun shugabannin jam’iyya, magoya baya da masu ruwa da tsaki da suka fito don shaida wannan muhimmin ci gaba.
"Wannan na daga cikin kokarin jam’iyyar na jawo jama’a a jiki tun daga matakin tushe domin a dama da su a harkokin siyasa."

- Hon. Saifullahi Hassan.

2027: Tinubu na duba yiwuwar jawo Kwankwaso

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu na duba yiwuwar maye gurbin mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima gabanin zaɓen 2027 da ke tafe.

Wasu majiyoyi masu ƙarfi na nuni da cewa shugaban ƙasar na tunanin jawo Kwa kwaso zuwa APC kuma ya ɗauke shi a matsayin abokin takararsa a 2027.

Majiyar ta ƙara bayyana cewa APC ta gano Kwankwaso na da matuƙar amfani saboda ƙwarewarsa da gagarumin farin jini da ya ke da shi a Arewacin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262