An Samu Karin Masu Son a Sauya Kashim, Kungiyar APC na Son Tinubu Ya Dauko Dogara
- Kungiyar APC ta Arewa maso Gabas ta jaddada goyon baya ga jagorancin Abdullahi Ganduje, a lokaci guda kuma ta mika bukata ga Bola Tinubu
- Shugaban kungiyar, Hon. Sha’abdini Bello, da sakataren, Barista Jerry Adamu sun mika bukatar a wata sanarwar bayan taro da aka fitar
- Suna ganin akwai bukatar shugaba Tinubu ya sauya abokin takara a 2027, inda su ke fatan za a maye gurbin Kashim Shettima da Yakubu Dogara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Gombe – Kungiyar North-East Coalition ta sake jaddada cikakkiyar biyayyarta ga jam’iyyar APC, tare da gabatar da shawarar sunan wanda ya dace da zama mataimakin shugaban kasa ga Bola Tinubu.
A cikin wani taro na kwanaki biyu da aka gudanar a jihar Gombe, kungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga jagorancin jam’iyya na kasa.

Source: Facebook
Punch News ta wallafa cewa a sanarwar da shugaban kungiyar, Hon. Sha’abdini Bello, da sakataren, Barista Jerry Adamu, suka rattaba wa hannu, ta bayyana cikakken goyon baya ga shugabancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Kungiyar APC ta yabi Abdullahi Ganduje
The Sun ta ruwaito cewa ya ce kungiyar ta bayyana cewa jagorancin Ganduje na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban jam’iyyar.
Ta ce:
“Mun sake jaddada cewa muna biyayya ga tsarin jam’iyya kuma muna goyon bayan jagorancin kasa karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Hadin kai da biyayya su ne ginshikan nasarar jam’iyyar.”
Kungiyar ta caccaki wasu da ta bayyana da suna 'masu kishin Arewa' tana zargin su da cewa suna da son rai, suna kokarin gina kansu a maimakon duba moriyar jam’iyya da kasa baki daya.
Kungiyar APC ta yabawa Bola Tinubu
Kungiyar ta jinjinawa Shugaba Bola Tinubu bisa kokarinsa na tabbatar da tafiyar da gwamnati bisa tsarin da ya kunshi kowa da kowa, tana mai bukatar a fadada wannan yunkuri.

Source: Facebook
Sun ce:
“Shugaban kasa ya tabbatar da cewa shi jagora ne na kare hakkokin kowane bangare, musamman kananan kabilu. Muna bukatar ya ci gaba da nada mutane masu hangen nesa da kishin kasa domin inganta ci gaba a fadin kasa.”
A wani mataki da zai iya tayar da muhawara a fagen siyasa gabanin zaben 2027, kungiyar ta bayyana Rt. Hon. Yakubu Dogara, tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, a matsayin wanda ya dace ya zama abokin takarar Bola Tinubu.
A cewar kungiyar:
“Jagorancinsa a majalisar wakilai ta takwas ya kunshi hadin kai da adalci. Ya nada wakilai daga kowanne jiha a Arewa maso Gabas da kuma daga dukkannin yankunan siyasa guda shida na kasar. Dogara shugaba ne nagari wanda kowa ya yarda da cancantarsa.”
2027: Ana ganin Tinubu zai dauko Kwankwaso
A baya, kun ji cewa ana hasashen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na duba yiwuwar sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaben 2027 mai zuwa.
Rahotanni sun ce maganar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ta samu karɓuwa sosai a tsakanin manyan jam’iyyar APC da ke son Tinubu ya samu nasara a wa’adin mulkinsa na biyu.
Wata majiya ta ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin shugaban kasa da Kwankwaso, kuma tsohon gwamnan Kano ya kai ziyarar sirri ga Tinubu domin ci gaba da shawara kan batun.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


