Rikici Ya Kare: Tinubu Ya Gana da Fubara, Wike da 'Yan Majalisar Rivers a Aso Villa
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da ministan Abuja, Nyesom Wike, Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar Jihar Rivers
- Wike, Fubara da ‘yan majalisar dokoki ta jihar sun gana da shugaban kasa a Aso Villa domin kammala sulhun da aka fara a tsakaninsu
- Sulhun ya biyo bayan dogon rikicin da ya kai ga dakatar da gwamna Fubara da kuma nada tsohon soja a matsayin shugaba na wucin gadi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ana rade radin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala sulhu tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike da Gwamna Siminalayi Fubara.
Sulhun ya biyo bayan wata ganawa ta musamman da shugaban kasar ya yi da dukkan ɓangarorin da abin ya shafa a fadar shugaban kasa da ke Abuja a daren jiya.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce akwai alamun an shawo kan rikicin siyasar Rivers gaba daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rikicin siyasar jihar Rivers ya daɗe yana ci gaba tsakanin Wike da Fubara kan ikon tafiyar da harkokin mulki, lamarin da ya ɓarke zuwa cikin majalisar dokoki ta jihar.
Yadda aka dakatar da Fubara a Maris
A cikin watan Maris, shugaban kasa Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Rivers sakamakon tsanantar rikicin siyasa.
A kan haka aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa, Ngozi Odu, da kuma dukkan 'yan majalisar dokokin jihar.
Shugaban kasar ya naɗa tsohon hafsan sojin ruwa, Ibokette Ibas, a matsayin wanda zai tafiyar da jihar har zuwa lokacin da zaman lafiya zai dawo.
Matakin da kotu ta dauka a rikicin Rivers
Rikicin siyasar ya kai har kotu, inda bangaren majalisar dokoki suka samu nasara a kotun koli, amma hakan ya kara jefa jihar cikin wani sabon rikici.
Bayan wannan hukunci, wasu daga cikin mambobin majalisar da ke goyon bayan Wike sun bayyana shirin su na tsige Gwamna Fubara daga mukaminsa, abin da ya kara dagula lamarin.
Punch ta wallafa cewa wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaida cewa tuni aka fara sasanta rikicin tun kafin ganawa da shugaba Tinubu.

Source: Instagram
An yi sulhu tsakanin Fubara da Wike
Majiyar ta bayyana cewa ganawar da aka yi da shugaban kasa a jiya ta kasance ne domin sanar da shi cewa an cimma matsaya ta sulhu.
“Daga yadda fuskokinsu suka nuna bayan fitowarsu daga ganawar da shugaban kasa, za a iya cewa sulhu ya tabbata. Sun bi umarnin shugaban kasa da ya bukaci a shawo kan rikicin,”
- Inji majiyar
Ana ganin cewa ziyarar wata alama ce ta godiya ga shugaban kasa bisa rawar da ya taka wajen sasanta bangarorin da rikicin ya raba.
Ana sa ran dawowar zaman lafiya a jihar Rivers bayan watanni da dama na tashe-tashen hankula da matsin lamba a tsakanin manyan shugabannin siyasa na jihar.
Jonathan ya yi magana kan Simi Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi magana kan dakatar da gwamna Simi Fubara.
Goodluck Jonathan ya soki shugaban kasa Bola Tinubu kan cigaba da dakatar da Fubara da ya yi alhali yana ikirarin kare dimokuradiyya.
A watan Maris da ya wuce ne shugaba Tinubu ya dakatar da Fubara bayan ganawa da shugabannin tsaro a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


