2027: Dalillai 5 da Ka Iya Sa Tinubu Ya Sauya Kashim Shettima a Matsayin Mataimaki

2027: Dalillai 5 da Ka Iya Sa Tinubu Ya Sauya Kashim Shettima a Matsayin Mataimaki

  • Ana rade-radin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai sauya mataimakinsa, Kashim Shettima kafin zaɓen 2027, saboda matsin lamba daga wasu
  • Wasu a Arewa ta Tsakiya da Kiristoci na matsa lamba, suna neman a ba su kujera ta mataimaki, su na cewa an dade ana muzgunawa yankin
  • Rahotanni sun nuna tasirin Sanata Shettima yana raguwa a cikin APC, hakan na iya zama barazana ga nasarar jam’iyyar a zaɓen gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tun kafin zaben 2027, ana ta rade-radin cewa rikici na neman ɓarkewa tsakanin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Rade-radin cewa shugaban ƙasa zai sauya Kashim Shettima ya kai kololuwa a tsakiyar watan Yunin 2027 wanda ya fara kaso rarrabuwar kawuna.

An kawo dalilai da ake ganin Tinubu zai sauya Shettima
Ana hasashen Tinubu ka iya sa ya sauya Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Punch ta ce wasu manyan jam'iyyar APC mai mulki sun ce za a sake duba kan kujerar gabanin zaben 2027 da ke tafe.

Kara karanta wannan

'Tinubu na mayar da Najeriya kamar Lagos': Sarkin Lafiya ya faɗi abin da suka gani a Ikko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin gwamnoni da harin kujerar Shettima

Wasu majiyoyi sun bayyana akwai dalilai guda biyar da ka iya sa Shugaba Tinubu ya sauya Shettima a matsayin abokin takararsa wanda ake zargin wasu gwamnoni na harin kujerar.

Daga cikin wadanda ake zargin akwai gwamnonin Gombe, Yobe, Kaduna da kuma gwamnan jihar Katsina wanda daga bisani suka musanta zargin.

Har ila yau, akwai manyan shugabanni daga Majalisar Tarayya da suma ake zarginsu amma tuni suka musanta haka.

Legit Hausa ta yi duba kan wasu abubuwa da ka iya sanya Tinubu sake tunani game da Kashim Shettima:

1. Kalubalen addini da ke gaban Tinubu

Wasu jagororin Arewa sun shawarci Tinubu, wanda Musulmi ne, da ya zabi Kirista daga Arewa a matsayin mataimaki a zaɓen 2027.

Sun ce hakan zai kawo nasara mai rinjaye, maimakon cigaba da tsarin Musulmi da Musulmi wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a 2023.

Kara karanta wannan

Mataimaki a 2027: Barau ya fadi shirinsa kan yin aiki da Shugaba Tinubu

A lokacin tunkarar zaɓen 2023, tsarin Musulmi-Musulmi ya janyo fushi daga ‘yan Najeriya da dama da kuma kungiyoyin addini.

Wasu dalilai da zai sa Tinubu sauya Kashim Shettima
Ana hasashen Tinubu zai sauya Kashim Shettima a 2027. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

2. Yunkurin yankin Arewa ta Tsakiya

Wasu daga yankin Arewa ta Tsakiya na ganin Tinubu ya ɗauko mataimaki daga yankinsu idan yana son goyon bayansu a 2027.

Kwanan nan, kungiyar North Central Renaissance Movement ta yi barazanar janye goyon baya idan ba a ba su wannan dama ba.

Sun gana da manyan mutane ciki har da tsohon mai ba da shawara kan tsaro, Aliyu Gusau da Onah na Abaji, suna kukan muzgunawa tsawon shekaru 65.

Ga jihohin Kiristoci na Arewa ta Tsakiya da ke fama da ‘yan ta’adda, samun wakilci a fadar shugaban kasa yana da matuƙar mahimmanci.

3. Zargin karancin tasirin Kashim Shettima

Rahotanni sun nuna cewa tasirin Shettima na raguwa, wanda zai iya janyo APC ta fuskanci barazana daga ‘yan adawa a 2027.

A baya an ji irinsu Hakeem Baba Ahmed wanda yake ofishin mataimakin shugaban kasa sun ajiye aiki bisa zargin cewa ba a daukar shawararsu.

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

Hakan ya sa har ila yau ake ganin wannan lamari na iya hana jam’iyyar samun kuri’un da ake buƙata domin nasara a zaɓe mai zuwa.

An fara magana kan sauya kujerar Shettima
Ana zargin Tinubu zai iya sauya Kashim Shettima a 2027. Hoto: Kashim Shettima.
Source: UGC

4. Tarihin sauya mataimakansa tun 1999

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya dade yana sauya mataimakansa lokacin da ya ke riƙe da muƙamin gwamnan Lagos.

An ce Tinubu ya sauya mataimakansa aƙalla guda uku daga shekarar 1999 zuwa 2007 da ya bar kujerar mulki, cewar BusinessDay.

Daga cikin wadanda Tinubu ya yi aiki da su a cikin shekaru takwas da ya yi a kan mulki sun hada da Bucknor Akerele, Femi Pedro da Abiodun Ogunleye.

Ana rigima a APC kan kujerar Kashim Shettima
Ana hasashen Tinubu zai iya sauya Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Facebook

5. Rashin tabuka komai a zaben 2023

Akwai masu ganin cewa a zaben 2023, APC ba ta samu kuri'an da ta sa rai a Borno da kuma jihohin da ke Arewa maso gabas.

Wasu na ganin Tinubu zai iya sauya Kashim Shettima duba da tasirinsa musamman a zaɓen 2023 da ta gabata.

Yankin Arewa maso Gabas da Kashim ya fito ba su zabi Tinubu sosai ba inda dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya fi shi farin jini a yankin.

Kara karanta wannan

Atiku ya tsokani Tinubu, ya hango ruɗani a ɓullar sabon 'abokin karatunsa'

Barau ya musanta neman kujerar Shettima

Kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan rade-radin cewa Bola Tinubu zai maye gurbin Kashim Shettima da shi.

Mataimakin shugaban majalisar ya bukaci matasa su mayar da hankali wajen mara wa Shugaba Tinubu baya a aikin ceto Najeriya.

Ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da manufofin da ya ce ya kawo domin habaka tattalin Najeriya da inganta rayuwar 'yan kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.