Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Kai Tsaye kan Atiku da El Rufai Masu Shirin Kifar da Shi a 2027
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana haɗakar ƴan adawa da ke shirin kayar da shi a 2027 a matsayin ƴan gudun hijirar siyasa
- Bola Tinubu ya buƙaci magoya bayansu su yi fatali da su, kada su tsaya ɗaga hankalinsu kan haɗakar wacce Atiku Abubakar ke jagoranta
- Har ila yau, shugaban ƙasa ya kare kansa daga zargin fara yaƙin neman zaɓe tun kafin hukumar INEC ta bayar da damar hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Nasarawa - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya roƙi magoya bayansa da su yi watsi da yunƙurin wasu manyan ƴan siyasa da ke shirin kifar da gwamnatinsa a zaɓen 2027.
Shugaba Tinubu ya bayyana jagororin adawa da ke shirin haɗaka a matsayin "‘yan gudun hijira na siyasa."

Source: Twitter
Tinubu ya bayyana cewa duk da ba ya da niyyar fara kamfen da wuri, babu ɗan siyasar da zai zauna idan aka fara gina ƙungiya domin kifar da shi daga mulki, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Ana shirin tarar wa Tinubu, INEC ta faɗi sababbin jam'iyyun da aka nemi rijista kafin 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haɗakar Atiku, El-Rufai ta fara jan hankalin Tinubu
Jawabin nasa ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyar jiga-jigan jam’iyyun adawa ke ƙara samun ƙarfi domin ƙwace mulki a 2027.
Cikin waɗanda ake danganta da wannan haɗaka akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi.
Sai kuma tsofaffin gwamnoni, Nasir El-Rufai (Kaduna), Rotimi Amaechi (Ribas), Rauf Aregbesola (Osun), tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, da tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami (SAN) da sauransu.
Duk da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ba ta buɗe fagen kamfe ba tukuna, Tinubu na ci gaba samun goyon baya daga ‘yan APC, abin da wasu suka kira da take dokar zaɓe da gangan.
Tinubu ya yi magana kan haɗakar ƴan adawa
Yayin wata ziyarar aiki ta yini guda da ya kai jihar Nasarawa, Shugaba Tinubu ya ce APC ta yi haka ne a matsayin martani ga ƴan adawar da suka fara shiri tun da wuri.
“Kada ku damu kanku game da su, su duka ‘yan gudun hijira ne na siyasa. Kada ku ba su mafaka,” in ji Shugaba Tinubu..
Shugaban kasa ya yaba da kokarin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wajen kawo ci gaba a jihar.

Source: Twitter
Gwamnatin Tinubu za ta tallafawa Nasarawa
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da marawa gwamnan baya domin samar da damarmaki da ci gaba mai ɗorewa a Nasarawa.
"Ina ganin himma da jajircewar A.A. Sule, yana ƙoƙarin amfani da dukiyar da ke hannunsa domin ci gaban jihar Nasarawa. Sule na kokari ne domin Bola Tinubu ma yana kokari.”
"Wadanda suka fara siyasa da wuri ta hanyar wannan haɗaka, kada ku bari su ɗauke maku hankali, ƴan fafutukar siyasa ne kawai.
"Fatan alheri ya zo. Sule yana kokari, kuma za mu tallafa masa a duk wani tsari da zai kawo cigaban jihar Nasarawa. Wannan ne abin da muka tsayu a kai.”
- Bola Tinubu.
Dangane da zargin fara kamfe da wuri, Shugaba Tinubu ya ce bai yi niyyar karya dokar zaɓe ba amma ba zai yiwu ya zura ido yana kallo ana haɗa kai don kifar da shi ba, Channels tv ta rahoto.
El-Rufai ya yi hasashen faɗuwar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Nasir El-Rufai ya yi ikirarin cewa babu wata dama da za ta ba Bola Tinubu nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tsohon gwamnan kuma ɗaya daga cikin jagororin haɗaka, ya ce taɓarɓarewar tattalin arziki da tsaro na cikin dalilin da za su hana Tinubu samun tazarce.
Nasir El-Rufa'i ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta fi ta Buhari lalacewa, duk da cewa da farko ya yi tsammanin zai yi abin azo a gani.
Asali: Legit.ng

