Ana Murnar kafa ADA, El Rufai Ya Hango Kalubalen da Za a Iya Fuskanta a INEC
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna alamar tambaya kan yiwuwar samun adalci daga wajen hukumar zaɓe ta INEC
- El-Rufai ya nuna cewa da wuya hukumar INEC ta yarda ta amince ta yi wa wata sabuwar jam'iyya rajista a karkashin Mahmud Yakubu
- Sabon jigon na jam'iyyar hamayya ta SDP ya ce shugabancin INEC ya sha bamban da na lokacin da aka yi wa jam'iyyar APC rajista
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana fargabar da jagororin ƴan adawa suke da ita kan hukumar INEC.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa shugabannin ƴan adawa na da shakku game da yiwuwar samun rajistar sabuwar jam’iyya ƙarƙashin jagorancin INEC ta yanzu.

Source: Facebook
El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Prime Time' na tashar Arise tv a ranar Litinin.

Kara karanta wannan
Shugabanni da jiga jigan PDP sun gana da INEC a Abuja, an ji abin da suka tattauna
Ƴan adawa sun ƙirƙiro ADA
Wasu daga cikin shugabannin ƴan adawa da ke shirin kafa haɗaka domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu sun riga sun miƙa buƙatar rajistar sabuwar jam’iyya mai suna ADA a gaban INEC domin shiga zaɓen 2027.
Wannan ƙawance na samun jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar tare da Nasir El-Rufai.
Wace fargaba El-Rufai yake da ita kan INEC?
Sai dai, a yayin hirar da aka yi da shi, El-Rufai ya bayyana cewa akwai shakku mai yawa a zukatan shugabannin ƴan adawa dangane da sahihancin INEC ƙarƙashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu wajen amincewa da rajistar sabuwar jam’iyya.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya kwatanta halin da ake ciki yanzu da lokacin da aka yi rajistar jam’iyyar APC a ƙarƙashin shugabancin tsohon shugaban INEC, Farfesa Attahiru Jega.
“Yawancinmu ba mu yarda cewa za a yi rajistar sabuwar jam’iyya a ƙarƙashin wannan shugabancin na yanzu ba, domin Mahmood Yakubu ba Jega ba ne, kuma Shugaba Tinubu ba Jonathan ba ne."
"Waɗannan sune mutanen da ke kan mulki lokacin da aka yi rajistar APC."
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
El-Rufai ya so ƴan haɗaka su ɗauki SDP
Duk da kafa jam’iyyar ADA, El-Rufai ya jaddada cewa SDP ce mafi dacewa da kasancewa dandali na haɗakar ƴan adawa, yana mai cewa jam’iyyar tana da tarihi, gadon siyasa, da kuma ƙima a zukatan mutane.
Ya ƙara da cewa idan an cimma matsaya kan jam'iyyar da za a kafa, shugabannin ƴan adawa za su iya barin tsofaffin jam’iyyunsu domin haɗewa ƙarƙashin jam’iyya ɗaya.
“Ina da yaƙinin cewa SDP ce mafi dacewa da zama dandalin haɗakar ƴan adawa saboda tana da tarihi, tana da gadon siyasa, tana da daraja a zukatan mutane, kuma kusan komai nata yayi. Ina ta kokarin shawo kan abokan aiki na da mu amince da hakan."
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya yi kalamai kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sare gwiwoyin Shugaba Bola Tinubu kan zaɓen 2027.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa mai girma shugaban ƙasan bai da wata dama ta samun nasara a zaɓen 2027 da ake tunkara.
Tsohon gwamnan ya nuna cewa ƴan Najeriya sun karaya da gwamnatin APC saboda kasa samar da ci gaban da ake buƙata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

