PDP Ta Nemi Tinubu Ya Yi Barka da Sallan Rage Farashin Fetur da Lantarki

PDP Ta Nemi Tinubu Ya Yi Barka da Sallan Rage Farashin Fetur da Lantarki

  • Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaban ƙasa, Bola Tinubu da ya sake duba tsare-tsaren da ta ce sun jefa ‘yan ƙasa cikin kunci
  • PDP ta ce ya kamata a rage farashin man fetur, kudin wutar lantarki da sauran abubuwan da ke ƙara wa al’umma wahala
  • Jam’iyyar ta ce Sallah na nuni da bukatar shugabanni su rungumi tsoron Allah da sadaukarwa ga ‘yan ƙasa baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yayin bukukuwan Sallah, jam’iyyar adawa ta PDP ta roƙi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta yi dubi na musamman kan farashin man fetur da kudin lantarki.

Baya ga haka, PDP ta ce ya kamata Bola Tinubu ya sake duba sauran abubuwan more rayuwa da ke tsananta rayuwar ‘yan ƙasa.

Kara karanta wannan

Hanyar samun tsira da abubuwan da limamin Arafa ya bayyanawa Musulmai

Tinubu ta yi kira ga Tinubu a ranar sallah
PDP ta bukaci Tinubu ya saukaka wa talakan Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|PDP Official
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne ya fitar da sanarwar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta bukaci gwamnati da ta sauya manufofinta da suka shafi tattalin arziki da rayuwar talakawa.

Jam’iyyar ta ce saura shekara biyu a wa’adin Tinubu, don haka lokaci ne da ya kamata ya mayar da hankali kan kyautata rayuwar al’umma tare da kankan da kai da tsoron Allah.

PDP ta nemi Bola Tinubu ya rage kudin fetur

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsadar man fetur da wutar lantarki, da kuma karin haraji a muhimman abubuwa na gurgunta tattalin arzikin mutane da kasuwanci a fadin ƙasa.

Ta bukaci shugaban ƙasa ya dauki matakin rage farashin abubuwan domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa da ke fama da matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kaya.

PDP ta bayyana damuwarta da cewa talauci da yunwa na ƙaruwa a tsakanin al’umma, lamarin da ke buƙatar sauya salo a jagorancin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa da Tinubu ya fadawa 'yan Najeriya a sakon barka da sallah

PDP ta zargi Tinubu ta kawo wahalar rayuwa.
PDP ta bukaci ya sauya tsare tsarensa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ta ce hakan na da muhimmanci musamman ta hanyar kawo sauƙi a farashin kayayyakin da ke shafar rayuwar yau da kullum.

PDP ta bukaci yi addu’a da nuna jajircewa

Jam’iyyar PDP ta kuma bukaci al’umma da kada su karaya da halin da ƙasar ke ciki, tana mai jaddada bukatar ci gaba da yin addu’a da kuma jajircewa wajen taimakon juna.

The Guardian ta wallafa cewa PDP ta ce lokaci ne da ya dace ‘yan Najeriya su dage da addu’o’i domin samun shiriya da fitowa daga halin da ake ciki, tare da dogara ga alherin Allah.

Ta ce duk da matsalolin tattalin arziki, tsaro da sauran ƙalubale da ƙasar ke ciki, bai kamata ‘yan ƙasa su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da kishin ƙasa da taimakon juna.

A ƙarshe, PDP ta taya al’ummar Najeriya murnar bikin Sallar Layya, tana fatan za a yi shagulgulan cikin lumana da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

'Yan kwadago sun yi wa Tinubu wankin babban bargo bayan cika shekara 2 a mulki

Tinubu ya yi wa 'yan kasa barka da sallah

A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya taya 'yan Najeriya murnar babbar sallah da aka yi a ranar Juma'a.

Shugaban kasar ya ce yana sane da halin da kasa ke ciki kuma matakan da ya dauka sun fara haifar da 'da mai ido.

Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su cigaba da mara masa baya wajen cimma nasara kan tsare tsaren da ya dauko a fadin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng