2027: Babban Sarki Ya Barke da Yi wa Tinubu Kamfen a Taron Babbar Sallah

2027: Babban Sarki Ya Barke da Yi wa Tinubu Kamfen a Taron Babbar Sallah

  • Sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya bukaci ’yan Najeriya da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin ya kammala wa’adin mulki na biyu
  • Ya bayyana hakan ne yayin bukukuwan Sallah a Iwo, inda ya kwatanta sauye-sauyen Tinubu da sadaukawar da Annabi Ibrahim ya yi wajen yanka dansa
  • Sarkin ya ce kuncin da ake ciki sakamakon gyare-gyaren gwamnati ne, amma ya bukaci ’yan kasa da su ci gaba da juriya don dawowar martabar ƙasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Sarkin Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya roƙi ’yan Najeriya da su bar Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adin mulki na biyu domin a samu ribar sauye-sauyen da aka fara.

Sarkin ya yi wannan jawabi ne a lokacin bikin sallar layya da aka gudanar a filin Idi na masarautar Iwo a jihar Osun.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun sojin Najeriya suka yi bikin sallah a fagen daga a Borno

Oba Akabi ya yi wa Tinubu kamfen
Oba Akanbi ya roki a marawa Tinubu baya a 2027. Hoto: Iwo Hub Land|Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa sarkin ya kwatanta matakan Tinubu da irin hadayar Annabi Ibrahim, wadda ake tunawa da ita a lokacin Sallah.

A cewar wata sanarwa da jami’in masarautar, Alli Ibraheem, ya fitar, Oba Akanbi ya ce irin matsin da ’yan Najeriya ke ciki a yanzu wata riba ce da za ta haifar da cigaba a gaba.

Sarkin Iwo ya ce Tinubu gwarzon gyara ne

Sarkin ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ɗauki matakan da wasu shugabanni a baya suka kasa ɗauka, yana mai cewa ya fi mayar da hankali wajen gyara ƙasa fiye da jin ƙorafe-ƙorafe.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Wasu daga cikin wadanda suka yi watsi da shi kafin ya hau mulki yanzu suna goyon bayansa saboda suna ganin amfanin gyare-gyarensa. A ƙarshe, za mu ci riba gaba ɗaya.”

Oba Akanbi ya kuma bayyana cewa Tinubu na yin gwagwarmaya da manyan kalubale da ke hana cigaban Najeriya, yana mai kira da a ƙarfafa masa guiwa wajen kammala salon mulkinsa.

Kara karanta wannan

Hanyar samun tsira da abubuwan da limamin Arafa ya bayyanawa Musulmai

Tinubu: Sarkin Iwo ya yabi cire tallafin mai

A cewar sarkin, cire tallafin mai da Tinubu ya yi wata jarumta ce mai kyau, kuma hakan zai taimaka wa ƙasa a gaba.

A cewarsa:

“Na roƙi ’yan Najeriya da su duba jiya da yau. Gyare-gyaren sun fara haifar da sakamako. Albashin ma’aikata ya ƙaru, farashin kayan abinci yana raguwa,”

Sarkin ya ƙara da cewa lokaci ne da ya dace da al’umma su zama jakadun gaskiya da ci gaba, inda ya bukaci kowa da ya mara wa Tinubu baya don ƙasa ta dawo da martabarta.

Oba Akanbi ya ce hanyoyin da Tinubu ya ɗauka za su dawo da martabar Najeriya, musamman idan ’yan ƙasa suka ci gaba da juriya da fahimtar da ake buƙata wajen gyaran ƙasa.

Oba Akanvi ya yabi cire tallafin mai
Oluwo na Iwo ya ce Tinubu gwarzo ne da ya cire tallafin mai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattauna da Mua'zu Usman

Wani matashi a jihar Gombe mai suna Mu'azu Usman ya ce ba laifi ba ne idan sarkin ya bayyana ra'ayinsa na sake zaben Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa da Tinubu ya fadawa 'yan Najeriya a sakon barka da sallah

Mu'azu Usman ya zantawa Legit cewa:

"Yana da yancin fadan ra'ayinsa, amma kuma ayyukan Tinubu ne ya kamata su saka a sake zaben shi ba rokon mutane ba.
"Idan ya yi aikin da aka ji dadi, kowa zai sake zaben shi ba sai an roki mutane ne ba."

Tinubu ya yi barka da sallah ga 'yan kasa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya 'yan Najeriya murnar babbar sallah.

Shugaban kasar ya bukaci a yi wa kasa addu'a tare da tunawa da mutanen garin Mokwa da ambaliya ta shafa.

Bola Tinubu ya bayyana cewa matakan da ya fara dauka sun fara aiki a Najeriya kuma nan gaba kadan komai zai daidaita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng