Gwamna Eno Ya Shiga Matsala Ƙasa da Awa 1 Bayan Ya Sauya Sheƙa daga PDP zuwa APC

Gwamna Eno Ya Shiga Matsala Ƙasa da Awa 1 Bayan Ya Sauya Sheƙa daga PDP zuwa APC

  • Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya fara rasa kwamishinoninsa ƙasa da awa ɗaya bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Kwamishinan ayyuka na musamman, Mista Ini Ememobong ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ba zai iya bin gwamnan zuwa PC ba
  • Ya ce duk da ya bar gwamnatin Fasto Umo Eno, zai ci gaba da girmama shi a matsayinsa na ɗan uwa, wanda ya aminta da shi har ya naɗa shi a muƙami

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Kwamishinan ayyuka na musamman da tashar jiragen ruwa ta Ibom, Mista Ini Ememobong, ya yi murabus daga muƙaminsa a gwamnatin Akwa Ibom.

Kwamishinan ya ɗauki wannan mataki ne ƙasa da sa'a guda bayan Gwamna Umo Eno ya sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance yau Juma'a.

Kara karanta wannan

Akwa Ibom: PDP ta yi babban rashi ranar Sallah, gwamna ya sauya sheka zuwa APC

Ememobong ya ajiye aiki a gwamnatin Akwa Ibom.
Kwamishina na farko ya yi murabus bayan Gwamna Eno ya koma APC Hoto: Pastor Umo Eno, Ememobong
Source: Facebook

Mista Ememobong ya tabbatar da ajiye muƙaminsa ne a wata wasiƙa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun dawowar dimokuraɗiyya a Najeriya a shekarar 1999, jam’iyyar PDP ce ke mulkin jihar Akwa Ibom.

Gwamma Eno ya gargaɗi kwamishinoninsa

Sai dai makonni biyu da suka gabata, Gwamna Eno ya gargadi mambobin majalisar zartarwar jihar cewa duk wanda ba zai bi shi zuwa APC ba ya yi murabus.

A wani taron majalisar zartarwa na jihar, gwamnan ya ce:

“Ba sabon abu bane kowa ya san ina shirin sauya sheƙa; idan akwai wanda har yanzu bai sani ba, to ban san dalili ba. Duk wanda ba ya so ya bi ni, yana da ‘yancin yin hakan, amma ba zai kasance cikin hadimai na ba.
"Da zarar na sanar da sauya sheƙa, ku tabbatar kun shirya yin murabus, domin ba za ku zauna a cikin gwamnatina ku na yin adawa da tafiyata ba. Ba barazana ba ce, haka abin yake.”

Kara karanta wannan

Bayan jita jita na yawo, Wike ya magantu kan masu juya akalar gwamnatin Tinubu

Kwamishina 1 ya yi murabus a Akwa Ibom

Bayan sauya sheƙar da Gwamna Eno ya yi a ranar Juma’a, Ememobong ya sanar da murabus daga muƙaminsa na kwamishina nan take.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa, tsohon kwamishinan ya ce ya yi murabus ne saboda bin umarnin gwamnan cewa duk wanda ba zai bi tafiyarsa ba ya ajiye aiki.

“A yau na miƙa takardar murabus ga gwamna domin bin umarninsa cewa duk wanda ba zai shiga tafiyarsa zuwa APC ba ya yi murabus.
"Duk da cewa ba zan iya tambaya ko sukar matakin da gwamna ya ɗauka ba, amma ni ba zan iya bin wannan tafiya ba," in ji shi.
Mista Ini Ememobong ya ajiye aikinsa a Akwa Ibom.
Kwamishinan ayyuka na musamman a Akwa Ibom ya ce ba zai bi gwamna zuwa APC ba Hoto: Ini Ememobong
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa wannan shawara da ya yanke ba za ta shafi dangantakarshi da gwamnan ba, wanda ya bayyana a matsayin dan’uwa kuma wanda ya nuna masa yarda.

“Na yi aiki da gwamna a matsayin dan’uwa, kuma ya ba ni dama na shugabanci ma’aikatu biyu masu muhimmanci. Zan ci gaba da girmama Mai Girma Gwamna Umo Eno, duk da na yi murabus," in ji shi.

Kara karanta wannan

An kaɗa hantar Shugaba Tinubu kan matsalar tsaro, da yiwuwar a kifar da APC a zaben 2027

Gwamna Eno ya ce manufar jam'iyyu 1

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Pastor Umo Eno, ya ce duka jam'iyyun siyasa manufarsu ɗaya.

Gwamnan ya kalubalanci duk ɗan Najeriya da ke ganin ba haka bane da ya nuna masa banbancin manufofin jam’iyyun siyasar kasar nan.

Umo Eno ya ce jam'iyyun siyasa tsani ne kawai da ake takawa domin a ci zaɓe amma bayan mutum ya yi nasara, zai zama shugaba ga kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262