Tsohon Gwamnan APC Na Shirin Ficewa Jam'iyyar? An Ji Gaskiyar Zance

Tsohon Gwamnan APC Na Shirin Ficewa Jam'iyyar? An Ji Gaskiyar Zance

  • Tsohon gwamnan jIhar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya fito ya yi magana kan jita-jitar da aka riƙa yaɗawa a kansa
  • Rochas Okorocha ya karyata cewa yana shirin tattara ƴan komatsansa domin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa ko kaɗan ba shi da wani shiri na barin jam'iyyar wacce ya jajirce wajen kafuwarta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya shirya barin jam'iyyar APC.

Rochas Okorocha wanda ya shekara takwas yana gwamna ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC.

Rochas Okorocha
Okorocha ya ce zai ci gaba da zama a APC Hoto: Rochas Okorocha
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce tsohon sanatan mai wakiltar Imo ta Yamma ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sam Onwuemeodo, ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar

Okorocha ya ƙaryata jita-jitar da aka yaɗa

Okorocha ya kuma musanta rahoton da aka wallafa kwanan nan da ke cewa ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin wata jam’iyya da ke neman mulki ta kowace hanya.

Ya bayyana cewa labarin ƙarya ne wanda masu adawa da shi suka ƙirƙira don ɓata masa suna, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

A cewarsa, kasancewarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar mai mulki, ba zai taɓa faɗin irin wannan magana game da jam’iyyarsa ba.

Ya ce idan yana da wata matsala da jam’iyyar, ba zai fitar da ita a kafafen sada zumunta ba.

Me Okorocha ya ce kan ficewa daga APC?

“Kimanin shekaru takwas bayan barin kujerar gwamna a jihar Imo, da kuma wasu shekaru bayan zama Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, har yanzu masu adawa da Rochas Okorocha ba sa iya bacci lafiya da idanuwansu biyu a buɗe."
“Tsawon kwanaki, suna yaɗawa a kafafen sada zumunta wani labarin ƙarya, suna jingina shi da ni cewa na ce ‘APC ba jam’iyyar siyasa ba ce yanzu, sai dai wata jam’iyya mai son karɓe mulki ko ta halin ƙaƙa'".

Kara karanta wannan

"Kai tsaye na gaya masa": Amaechi ya fadi abin da ya gayawa Tinubu kan zaben 2023

"Okorocha ba zai taɓa kiran jam’iyyar da ta kasance a mulki tun daga 2015 har yanzu, da cewa tana ƙoƙarin karɓe mulki ba. Wane mulki kuma take ƙoƙarin karɓa?”
"Okorocha na nan daram a matsayin cikakken memba mai kishin APC. Bai taɓa furta irin wannan kalma da masu hassada da siyasarsa suke yaɗawa ba."

- Rochas Okorocha

Rochas Okorocha
Rochas Okorocha ya musanta shirin ficewa daga APC Hoto: Rochas Okorocha
Source: Twitter

Okorocha ya ƙara da cewa shi ne kaɗai gwamna daga Kudu maso Gabas da ya shiga APC tun lokacin kafuwarta, hakan ya sa ya kusa yin rashin nasara a zaɓen 2015, a lokacin da jam’iyyar ba ta da karɓuwa a yankin.

Tsallake a duniyar siyasar Najeriya

A Najeriya, sauya jam’iyya tsakanin ’yan siyasa ya zama ruwan dare, musamman idan ya shafi manyan shugabanni ko masu ruwa da tsaki a harkokin mulki.

Wannan al’ada ta sauya jam’iyya ba wai sabuwa ba ce, kuma galibi ba ta da nasaba da akidar siyasa ko manufar ci gaban al'umma, sai dai galibi tana shafi burin mutum na samun matsayi ko kariya ta siyasa.

Yawancin ’yan siyasa a Najeriya na sauya jam’iyya ne idan sun ji ba su da cikakken rinjaye ko kariya a inda suke, ko kuma idan sun ga wata dama ta fiye musu a wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

Kudin mazaɓa: Tinubu ya ba kowane ɗan Majalisar Tarayya Naira biliyan 1? Bayanai sun fito

Hakan ya sa mutane da dama ke ganin cewa siyasa a Najeriya ba ta da akida, illa kawai neman mulki da kariya daga hukunci ko gazawa.

Sabanin kasashen da akida da tsarin jam’iyya ke taka muhimmiyar rawa, a Najeriya sau da yawa mutum zai iya kasancewa memba a jam’iyya guda yau, gobe kuma ya koma wata ba tare da wata matsala ko kunya ba.

Wannan yanayi ya sa mutane da dama suka rasa amincewa da ’yan siyasa, saboda ana kallon su a matsayin masu son kai fiye da ci gaban kasa.

Wannan matsala ta sa sau da yawa ana yada jita-jita game da shirin wasu ’yan siyasa na barin jam’iyyarsu, kamar yadda aka gani a lamarin Rochas Okorocha.

Gidan Sanara Okorocha ya ruguje

A wani labarin kuma, kun ji cewa gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ruguje a birnin tarayya Abuja.

Gidan na Rochas Okorocha ya ruguje ne a yankin titin Ahmadu Bello Way da ke a cikin birnin tarayya Abuja.

Ginin ya rufto ne lokacin da ake gyaran gidan wanda hakan ya jefa mutanen da ne zaune a unguwar a cikin firgici.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng