Taraba: 'Yan APC Sun Shiga Tsaka Mai Wuya bayan Karɓar Muƙamai a Gwamnatin PDP

Taraba: 'Yan APC Sun Shiga Tsaka Mai Wuya bayan Karɓar Muƙamai a Gwamnatin PDP

  • Ba tare da wata-wata ba, jam’iyyar APC mai adawa a jihar Taraba za ta hukunta ‘ya’yanta da suka karɓi mukami daga gwamnatin PDP
  • Shugaban APC na jihar, Ibrahim El-Sudi, ya ce ba wanda zai tsira idan ya karɓi mukami ba tare da amincewar kwamitin ƙoli na jam’iyyar ba
  • El-Sudi ya umurci shugabannin kananan hukumomi da na mazabu su binciki lamarin, su kuma cire sunayen wadanda suka amince da mukaman gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jalingo, Taraba - Jam’iyyar APC reshen Jihar Taraba ta gargadi ƴaƴanta da suka karbi mukamai a gwamnatin Agbu Kefas.

Jam'iyyar mai adawa ta umurci a cire sunayen mambobinta da suka karɓi mukaman siyasa daga gwamnatin PDP ta Gwamna Kefas.

An gargadi jiga-jigan APC a Taraba
APC za ta kori mambobinta da ke cikin gwamnatin Agbu Kefas. Hoto: Agbu Kefas, Ibrahim Tukur El-Sudi.
Source: Facebook

APC ta gargadi mambobinta a Taraba

Shugaban APC na jihar, Barista Ibrahim Tukur El-Sudi shi ya fitar da wannan sanarwa ga yan jaridu, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

An 'bankado' yadda APC ke firgita 'yan adawa, tana jawo su cikinta karfi da yaji

El-Sudi ya yi gargaɗin cewa babu wanda zai tsira idan ya karbi mukami ba tare da izini ba.

Ya ce sun ankara da yawa daga mambobin jam'iyyar suna karɓar mukamin gwamnatin Kefas ba tare da tuntubar su ba.

A cewarsa:

“Mun lura da yadda Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ke ba da mukamai ga ‘ya’yan jam’iyyarmu ba tare da tuntubar shugabancin jam’iyya ba.
“Bincikenmu tare da Kwamitin Gudanarwa da Hedikwatar Jam’iyya ta kasa ya nuna babu wani izini da aka bayar a yi hakan.
“Dangane da Sashe na 9.5 na kundin tsarin mulkin jam’iyya, wanda aka yi wa gyaran fuska a 2022, hakan na nufin mutum ya fita daga jam’iyya.”
Ana zargin wasu yan APC a cikin gwamnatin PDP
APC za ta soke sunayen mambobinta da ke da muƙami a gwamnatin Taraba. Hoto: Agbu Kefas.
Source: Twitter

Matakin da APC ta shirya dauka kan mambobinta

El-Sudi ya ce idan har suka gane mutum ya karbi muƙamin babu izinin jam'iyyar APC, za su tabbatar da hukuncin kansa, cewar Daily Post.

Jam’iyyar ta ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Atiku: "Talakawa za su kada kuri'ar raba gardama kan gwamnatin Tinubu"

“Mutum zai rasa matsayinsa na mamba idan ya karbi mukami daga wata jam’iyyar gwamnati ba tare da amincewar jam’iyyar ba.
“Da zarar mutum ya fita daga jam’iyyar, wajibi ne ya dawo da duk wasu kadarorin jam’iyyar da ke hannunsa."

Sanarwar ta umurci shugabannin mazabu da su cire sunayen waɗanda suka karbi mukami daga gwamnatin jihar Taraba daga rajistar jam’iyya.

“Hakanan shugabannin APC na kananan hukumomi su binciki jerin sunayen waɗanda aka ba mukamai, domin tabbatar da ko sun karɓa ko a’a."

- Cewar El-Sudi

Jigon APC ya ki karbar mukami

A baya, kun ji cewa dan gwagwarmaya, Rikwense Muri a jihar Taraba, ya ki karbar muƙami da Gwamna Agbu Kefas ya ba shi a matsayin hadimi kan ayyuka.

Muri, wanda dan jam’iyyar APC ne, ya ce ya ki karbar nadin ne bayan tuntuba da shugabannin siyasa da jama’arsa saboda dalilai daban-daban.

Ya yaba da kokarin Gwamna Kefas na jawo kowa a mulki, amma ya ce ya amince ga manufofin jam’iyyar APC da shugaba Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.