Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

  • Wasu mutane dake bauta a wani coci a jihar Taraba sun rasa rayukansu sakamakon rugujewar cocin
  • An ruwaito cewa, a kalla mutane biyu suka mutu yayin da da dama suka jikkata suke karbar kulawar likita
  • Shugaban karamar hukumar Takum ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana mai yiwuwa don taimakawa wadanda suka jikkata

Taraba - Ginin coci ya ruguje a jihar Taraba, inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata masu ibada da dama.

Rahoton da muka samu ya ce Cocin na Holy Ghost Church, yana cikin garin Chanchanji ta karamar hukumar Takum ta jihar.

Shugaban karamar hukumar Takum, Shiban Tikari ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Asabar da gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1

Labari da duminsa: Coci ya ruguje kan masu bauta a jihar Taraba
Cocin da ya ruguje a jihar Taraba | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wadanda abin ya rutsa da su - Demenege James da Mwueze Terzunwe - an ce suna ibada a cocin da ke kauyen Peva kafin ginin ya tsage.

Ya bayyana cewa wadanda suka jikkata suna karbar magani a cibiyar kula kiwon lafiya ta makakin farko a yankin.

Korar minostocin Buhari: APC ta ce a maye gurbin Sale Mamman da dan jihar Taraba

Jam'iyyar APC mai ci a jihar Taraba ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bai wa jihar mukamin minista a madadin tsohon ministan wutar lantarki Sale Maman wanda aka cire kwanan baya.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Ibrahim El-Sudi ne ya yi wannan kiran lokacin da yake zantawa da Daily Trust a Jalingo ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu

Ya ce Taraba ta cancanci mukamin minista saboda jihar jiha ce da APC ke mulka.

El-Sudi ya bayyana cewa APC a jihar ta bai wa shugaba Buhari kuri'u sama da kashi 45 cikin dari a lokacin zaben shugaban kasa da ya gabata.

NEDC ta fara gina makarantu ga talakawa a yankunan da Boko Haram ta addaba

A wani labarin, Hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) ta fara gina karin makarantu a jihar Yobe, da sauran sassan arewa maso gabas, a matsayin wani mataki na magance karuwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin.

Manajan Daraktan Hukumar, Mohammed Alkali ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a Gasua, jihar Yobe, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Ya ce rikicin Boko Haram ya lalata makarantun firamare da na sakandare a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel