Atiku: "Talakawa za Su Kada Kuri'ar Raba Gardama kan Gwamnatin Tinubu"
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce ‘yan Najeriya za su yanke hukunci kan gwamnatin Bola Tinubu
- Ya bayyana haka ne a lokacin da APC ta zarge shi da kokarin farfado da adawa saboda ya cimma manufar kashin kansa
- A martaninsa, Atiku ya ce yanzu haka Najeriya ta zama matattarar talauci da fatara da rashin bunkasar tatttalin arziki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zaben 2027 zai zama tamkar kuri’ar raba gardama da za ta tantance yadda gwamnatin Bola Tinubu ta gudanar da mulki.
Jam’iyyar APC ta soki Atiku, tana zarginsa da kokarin sake farfado da ‘yan adawa ne don cimma burin kansa, tare da neman samun damar komawa kan dukiyar gwamnati.

Source: Facebook
Vanguard ta ruwaito cewa a martaninsa, mai magana da yawun Atiku, Mazi Paul Ibe, ya karyata wadannan zarge-zargen da APC ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya kare kansa daga zarge-zargen APC
Jaridar Daily Post ta kuma ruwaito cewa Ibe ya ce yunkurin Atiku yana gudana ne bisa bukatar ‘yan Najeriya na samun rayuwa mai inganci.
A cewarsa:
“A bayyane yake cewa ba su shirya mulki ba tun farko. Abin da ke gabansu kawai shi ne siyasa. Sun kai makura wurin hana ci gaban kasa. Kowanne matakin da suke dauka yana cin karo da tsarin dimokuradiyya."
Atiku ya ga gazawar gwamnatin Bola Tinubu
Ibe ya bayyana gazawar gwamnatin Tinubu, wanda ya danganta da rashin kwarewa wurin gudanar da aiki.
Ya bayar da misali da yadda aka kammala hanya mai kilomita 30 kacal daga cikin kilomita 700 cikin shekaru biyu.

Source: Facebook
Ya ce:
"Sun buga ganguna suna murnar kammala 4% na aikin. Wannan ba raini ba ne? Wannan rashin da’a ne! Kudin da aka kashe wajen murnar ma ya isa a kara gina wasu kilomita da dama."
'Najeriya ta zama cibiyar talauci' - Atiku
Hadimin Atiku Abubakar ya ce halin da ake ciki a Najeriya ya tabarbare matuka, inda ya bayyana cewa kasar na kan gaba wajen talauci da kuma rashin abinci ga yara a Afrika.
A cewarsa:
“Mutane na cikin yunwa. A karo na farko, za ka iya kirga wadanda za su iya siyan rago domin Sallah da yatsunsu. An ce ma wasu na hada kudi ne gaba daya domin siyan rago guda su raba."
“Zabe mai zuwa zai kasance tsakanin Tinubu da sauran ‘yan Najeriya.”
Jam'iyyar APC ta yi kaca-kaca da su Atiku
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar mai mulki ta APC ta caccaki manyan 'yan siyasa Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi, saboda sun ce akwai yunwa a kasa.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran APC na kasa, Felix Morka, ya fitar, jam'iyyar ta ce su Atiku, El-Rufai da Amaechi sun rike manyan mukamai a kasar nan.
Ya ce duk da sun rike madafun iko a Najeriya daga 1999 zuwa 2023, amma sun kasa magance matsalolin tattalin arziki da talauci da ya damu jama'a a mulkinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

