APC Ta Haɗa Atiku, El Rufa'i da Amaechi, Ta Yi Masu Kaca Kaca saboda Taba Tinubu

APC Ta Haɗa Atiku, El Rufa'i da Amaechi, Ta Yi Masu Kaca Kaca saboda Taba Tinubu

  • Kalaman manyan 'yan adawa a kasar nan a kan salon mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu bai yiwa jam'iyya mai mulki dadi ba
  • APC ta zargi Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufa’i hadewa wuri guda kawai domin kishin aljihunsu ba talakawa ba
  • Jam'iyyar ta ce su uku sun gaza a shekaru 24 da suka yi a mulki, inda ta zarge su da hannu a cefanar da kadarorin kasa ga daidaikun jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Jam’iyyar APC ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i.

Yayin da suke sukar mulkin Bola Tinubu, APC ta zargi manyan 'yan siyasar uku da neman komawa kan mulki ne domin amfanin kansu ba don jama’a ba.

Kara karanta wannan

'Duk mun koma mayunwata': Tsohon minista ya fadi abin da ke jiran Tinubu a 2027

Tinubu
APC ta soki Atiku, El Rufa'i da Amaechi Hoto: Nasir El Rufa'i/Atiku Abubakar/Bayo Onanuga
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa APC ta ce yan siyasan dake sukar manufofin tattalin arzikin shugaban Bola Tinubu yayin bikin cika shekara 60 na Amaechi na fafutukar su dawo siyasa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ake tattaunawa a taron, Rotimi Amaechi ya ce 'yana jin yunwa', yana mai sukar halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu.

Jam'iyyar APC ta yi kaca-kaca da su Atiku

Punch News ta wallafa cewa a wata sanarwa da Felix Morka, sakataren yada labarai na kasa na APC na kasa ya fitar a ranar Litinin, ya soki su Atiku da abokansa.

Ya ce ba su da bakin da za su zargi Tinubu da rashin iya magance talauci, alhali su ma sun kasa yin hakan kusan shekaru 25 da suke fagen mulki a kasar nan.

Morka ya ce:

“Jam’iyyar APC tana musanta cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ‘amfani da talauci a matsayin akalar juya talaka’ saboda ba ta magance matsalar cikin shekaru biyu ba— abin da su da kansu suka kasa cimma a kusan rabin karni suna kan mulki.”

Kara karanta wannan

'Yadda za mu kwace mulki daga hannun Tinubu a 2027,' Atiku, El Rufai sun magantu

Ya ce taron tunawa da ranar haihuwar Amaechi ya koma wani taron mutanen da suka yi watsi da damar da suka samu a lokacin da suke mulki,.

APC: 'Atiku, El-Rufai da Amaechi sun gaza'

APC ta ce su Atiku da abokansa sun rike manyan mukaman mulki a kasar nan tun daga 1999 zuwa 2023, amma ba su tabuka abin kirki ba wajen magance matsalar talauci a jihohinsu ba.

Tinubu
APC ta ce manyan yan siyasar ba su da bakin sukar Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewar Morka:

“Dukkaninsu sun rike manyan mukaman siyasa tun daga 1999 har zuwa 2023. A cikin wadannan shekaru 24, kowannensu bai iya kawar da talauci a jiharsa ko kasa baki daya ba.
“Ba ma sun yi kokarin magance matsalolin da ke hana ci gaban tattalin arziki ba, balle su fuskanci matsalolin tsarin da ke kara jefa mutane cikin yunwa da fatara.”

Ya kara da cewa waɗannan ‘yan siyasa na da hannu wajen “sayar da kadarorin kasa ga jawo asarar kudin jama’a da kuma daukar nauyin tashin hankali a matakin jihohi.

An zargi gwamnatin APC da jawo wahalhalu

A wani labarin, mun wallafa cewa kungiyar ci gaban Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta gaza cika alkawuran da ta daukar a 2023.

Kara karanta wannan

'Akwai babbar barazana ga APC,' Babban lauya ya fadi abin da zai kifar da Tinubu

Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Oba Oladipo Olaitan, da sakataren yada labaran ƙasa, Justice Faloye, suka fitar a ranar Lahadi, inda ta ce gwamnati ta gaza.

A cewar kungiyar, rahoton rabin wa’adin gwamnatin Tinubu ya nuna cewa Najeriya ta koma baya a kowane fanni, tun daga tattalin arziki, siyasa, har zuwa ci gaban bil’adama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng