"Na Faɗa Masa," Sanata Ya Buƙaci Tinubu Ya Kori Wasu Ministoci da Hafsoshin Tsaro

"Na Faɗa Masa," Sanata Ya Buƙaci Tinubu Ya Kori Wasu Ministoci da Hafsoshin Tsaro

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana cewa akwai bukatar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori wasu ministoci da hafsoshin tsaro
  • Kalu, tsohon gwamnan jihar Abia ya ce ya faɗa wa Bola Tinubu a sirrince cewa wasu daga cikin mutanen da ya naɗa ba su cancanta ba
  • A watan Oktoba, 2024, Shugaba Tinubu ya sallami wasu daga cikin ministocinsa, ya kuma canza wa wasu wuraren aiki a majalisar FEC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, ya shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauke wasu ministoci.

Sanata Kalu ya buƙaci Shugaba Tinubu ya sallami wasu daga cikin hafsoshin tsaro, yana mai cewa ba su da wani tasiri kuma sun gaza samar da ci gaba ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata ya fadi yadda ake kara karfin Boko Haram don dagula mulkin Tinubu

Sanata Orji Kalu.
Sanata Orji Kalu ya bukaci Shugaba Tinubu ya sauke wasu ministoci da shugabannin tsaro Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Twitter

Orji Kalu, wanda tsohon gwamnan jihar Abia ne, ya bayyana hakan ne a wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels mai suna Politics Today a daren Litinin.

Kalu ya buƙaci Tinubu ya kori wasu ministoci

Ya ce ya yi nazari da kimanta ayyukan ministocin gwamnatin Tinubu, kuma ya fahimci akwai waɗanda ya kamata a kora daga aiki.

“Wasu daga cikin mutanen da ke aiki tare da Shugaba Tinubu bai kamata su ci gaba da zama a kujerunsu ba.
"Wasu daga cikinsu a ɓangaren tsaro da ministoci, ya kamata a sallame su daga aiki," in ji Kalu.

Sanata Kalu ya kuma bukaci shugaba Tinubu da ya dauki sahihin matakai masu kyau, yana mai cewa akwai bukatar sauyi domin cika burin ‘yan Najeriya.

Waxu hafsoshin tsaro ya kamata Tinubu ya kora?

Kalu ya ce:

“Ya kamata Shugaba Tinubu ya samu ƙwarin gwiwa, ya sallami wasu daga cikin ministocin nan. Na riga na yi masa bayani a sirrance, kamata ya yi a kori mafi yawa daga cikinsu."

Kara karanta wannan

Matashi ya saya wa Tinubu ragon layya, ya yi wa mamar shugaban kasa mai suna

Dangane da tsaro kuwa, Orji Kalu ya ce akwai bukatar sauya wasu manyan hafsoshin tsaro saboda gazawarsu wajen shawo kan kalubalen da kasa ke fuskanta.

“Idan ya dauki shawarata, wasu daga cikin shugabannin tsaro ma za su tafi. Babu maganar son zuciya idan har muna son ceton Najeriya,” in ji shi.
Kalu da Tinubu.
Sanata Kalu ya ce mafi yawan ministocin Tinubu ba su cancanta ba Hoto: Senator Orji Kalu
Source: Facebook

Yadda Tinubu ya tsige ministoci a baya

Tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaba Tinubu ya nada ministoci 45, mafi yawa a tarihin Najeriya tun bayan dawowar dimokuraɗiyya a 1999.

Wannan yawan adadi na ministoci ya jawo ce-ce-ku-ce da martani daban-daban daga ‘yan kasa, kamar yadda Punch ta rahoto.

A watan Oktoba 2024, Shugaba Tinubu ya yu garambawul a majalisar ministoci, inda ya sallami ministoci biyar, ya nada sababbi bakwai, sannan ya canza wa mutum 10 wurin aiki.

Fadar shugaban ƙasa ta kare batun karɓo bashi

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske kan basussukan da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ke shirin karɓowa.

Fadar shugaban ƙasan ta ce tsarin karɓar bashi da gwamnati ke yi, abu ne da za a iya cewa ya zama dole don ci gaban tattalin arziƙi.

A makon da ya gabata, Shugaba Bola Tinubu ya aike da bukata zuwa majalisar tarayya domin neman amincewa da ƙarin bashi a ciki da wajen ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262