Wike Ya Cika Baki kan Batun Korarsa daga PDP, Ya Kalubalanci Jiga Jigan Jam'iyyar

Wike Ya Cika Baki kan Batun Korarsa daga PDP, Ya Kalubalanci Jiga Jigan Jam'iyyar

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa zai ci gaba da zama daram a cikin jam'iyyar PDP
  • Wike ya bayyana cewa babu wanda ya isa ya kore shi daga jam'iyyar wanda ya ɗauki tsawon shekaru ya na yi wa hidima
  • Ministan ya kuma musanta zargin cewa ya ci amanar PDP a zaɓen 2023 saboda goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da ya yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya mayar da martani ga masu kira da a kore shi daga jam’iyyar PDP.

Wike ya bayyana cewa babu wanda ke da iko ko ƙarfin halin da zai iya korarsa daga jam’iyyar PDP wadda ya yi wa hidima na tsawon shekaru.

Nyesom Wike
Wike ya ce ba a isa a kore shi daga PDP ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike -CON, GSSRS
Source: Facebook

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Bayan tsokano manya a Abuja, Wike ya fadi abin da yaƙe sanya shi farin ciki

Nyesom Wike zai ci gaba da zama a PDP

Ministan na birnin tarayya Abuja ya kuma tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a cikin jam'iyyar PDP, rahoton The Nation ya tabbatar.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana a fili cewa biyayyarsa ga PDP na nan daram, kuma ba za a iya korarsa cikin sauƙi ba.

"Har yanzu ina cikin PDP. Na yi aiki tuƙuru don jam’iyyar. Ban ga wanda zai iya ce min, ‘Wike, kai ba mamba ba ne na jam’iyyar’. Waye shi? Wace gudunmawa ya bayar ga jam’iyyar da ta fi nawa?”

- Nyesom Wike

Wike ya kare kansa daga yi wa PDP zagon ƙasa

Nyesom Wike ya kuma jaddada cewa bai taɓa cin amanar jam’iyyarsa ba, duk da ya marawa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen shekarar 2023.

Nyesom Wike
Wike ya ce bai ci amanar PDP ba Hoto: @GovWike
Source: Facebook
“A shekarar 2023, ba na gaya muku cewa ba zan goyi bayan ɗan takararsu na shugaban ƙasa ba? Na ce bisa gaskiya, adalci da daidaito, kamata ya yi shugaban ƙasa ya koma Kudu, domin ba za ku iya riƙe shugabancin ƙasa da na jam’iyya gaba ɗaya a lokaci guda ba."

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya raba hanya da Tinubu da Ganduje, ya fice daga jam'iyyar APC

"Ku ɗauki daya, ku bar mana ɗaya. Saboda sun yi imani cewa Atiku zai ci, sai suka ce mu yi duk abin da za mu yi, mu kuma muka ce ba za mu mara masa baya ba.”
“To me ya sa ban bar jam’iyyar ba na koma APC? Daga cikinmu a wancan lokacin da kuma gwamnonin PDP na yanzu, wa ya kawo dukkan kujerun ƴan majalisun tarayya ? Wa ya samar da gwamna? Ku tambaye su a jihohinsu, sanatoci nawa suka samu?”

- Nyesom Wike

Wike na jin daɗin taka manyan mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana jin daɗin taka manyan mutane.

Wike ya bayyana cewa dole ne duk wani mai wata kadara a birnin Abuja ya biya kuɗin harajin fili ko kuma ya fuskanci hukunci.

Ministan ya nuna cewa babu wani babba da yake jin kansa da zai ɗaga wa ƙafa kan batun biyan kuɗaɗen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng