Kalaman Ministan Buhari kan 'Yunwa' Sun Fara Rikita na Kusa da Tinubu, Wike Ya Ɗauki Zafi
- Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya caccaki tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi kan kalaman da ya yi game da yunwa
- Tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa babu yunwar abinci a tattare da Rotimi Amaechi, sai dai yunwar samun mulki
- A makon jiya Amaechi ya yi ikirarin cewa kowa na fama da yunwa a ƙarƙashin mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya maida martani ga tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, bisa kalamansa na cewa, "an maida mutane mayunwata."
Wike ya bayyana cewa ba yunwar abinci ke damun, Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas ba, sai dai yunwar muki.

Source: Facebook
Nyesom Wike ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, 2 ga watan Yuni, 2025, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar
Ministan, wanda shi ma tsohon gwmanan jihar Ribas ne ya yi ikirarin cewa yunwar mulki ke damun Amaechi, ba yunwar abinci ba kamar yadda ya furta.
Abin da Rotimi Amaechi ya faɗa kan yunwa
Tun farko dai a wurin bikin cikarsa sheksra 60 a duniya, Amaechi ya yi tsokaci kan halin da ƴan Najeriya ke ciki na yunwa da taɓarɓarewar tattalin arziki a mulkin Shugaba Tinubu.
Amaechi, wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce:
“Muna jin yunwa, kowa ya zama mayunwaci. Idan kai ba ka ji, ni dai ina jin yunwa. Mu ƴan adawa, idan muka zage damtse, za mu iya cire shi daga kan mulki."
Wike ya mayar da martani ga tsohon minista
Sai dai ga dukkan alamu waɗannan kalamai ba su yi wa Wike daɗi ba, wanda ya fito ya maida martani da cewa:
“Ba mu da lokacin sauraren shirme a Najeriya. Na rasa gane taya mutum irin Amaechi zai zauna a ranar cikarsa shekara 60 yana yaudarar ’yan Najeriya da cewa yana jin yunwa.”
“Ya kasance Kakakin Majalisar jiha daga 1999 zuwa 2007, Gwamna daga 2007 zuwa 2015, sannan Minista daga 2015 zuwa 2023. Ko da yaushe yana rike da mukami, bai taba ambaton yunwa ba.”
“Yanzu da ya rasa mulki, sai ya dawo yana cewa yunwa. Wannan yunwar ba ta abinci ba ce, yunwar mulki ce.”

Source: Twitter
Wike ya soki haɗakar Amaechi da Atiku
A rahoton The Nation, Wike ya ce wannan magana ta nuna gazawar Amaechi, inda ya ci gaba da cewa:
"Yanzu sun dawo suna sake haɗe kai, wannan ya nuna gazawarsa, taya zaka kawo batun ƙabilanci game da yunwa? Ya haɗa kai da Atiku suna ikirarin yunwa, an yi walƙiya mun gane ba zai iya zama ba mulki ba."
"Bari mu zuba ido mu ga yadda za su cire shugaban kasa daga mulki. Ko ta hanyar juyin mulki ne? Kalmar ‘cirewa’ alama ce ta danniya ko juyin mulki.”
Ministan Abuja ya kafe kan batun harajin fili
A wani labarin, kun ji cewa Nyesom Wike ya bayyana cewa yana matuƙar jin daɗin taka manyan mutane da suke ganin sun fi ƙarfin doka.
Ministan ya jaddada cewa babu wanda zai ɗaga wa ƙafa kan batun biyan harajin fili a babban birnin tarayya Abuja, duk girmansa kuma duk da matsayarsa.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya soki wasu jiga-jigan PDP ciki har da Bode George, ya ce dole ne PDP ta biya kuɗin harajin filin da sakatariyarta ke kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

