Zaben 2027: Kungiyar Shekarau Ta Gindiya Sharadi kafin Shiga Hadakarsu Atiku
- Ƙungiyar LND ta Ibrahim Shekarau ta bukaci su Atiku Abubakar su kafa sabuwar jam’iyya kafin su shiga kawancen ‘yan adawa a 2027
- Dr. Umar Ardo, shugaban kungiyar ya ce bai kamata ayi amfani da tsofaffin jam’iyyu kamar ADC da SDP ba saboda gudun rikicin shugabanci
- LND ta yi bayani cewa sabuwar jam’iyya za ta zo da sababbin akidu, tsari mai inganci da kuma ƙarfin jawo hankalin ‘yan Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ƙungiyar LND ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau, ta bukaci su Atiku Abubakar su kafa sabuwar jam’iyyar hadaka.
LND ta shaida cewa kafa sabuwar jam'iyar ne sharadin shigarta kawancen ‘yan adawa da ke ƙoƙarin kawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Source: Facebook
LND ta kafa sharadin shiga hadakarsu Atiku
Shugaban LND, Dr. Umar Ardo, tare da wasu manyan mambobi 12 na ƙungiyar, suka bayyana haka a sanarwar da suka fitar bayan nazari kan zabin da ke gaban kwamitin kawancen, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni na nuna cewa ana sa ran wannan kawance, wanda Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan siyasa irin su Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi ke jagoranta, zai yi amfani da jam’iyyar ADC ko SDP domin fafatawa da APC a zaben 2027.
Sai dai a cikin sanarwar da Ardo ya fitar a jiya Lahadi, ya ce:
“Bayan nazari mai zurfi kan zabin kafa sabuwar jam’iyya ko haɗewa da wacce aka rigaya aka yi wa rajista kamar ADC ko SDP, mun yanke shawarar cewa kafa sabuwar jam’iyya ce hanya mafi nagarta, gaskiya da ɗorewa ga nasarar ‘yan adawa.”
Dalilin LND na son a kafa sabuwar jam'iyya
Dr. Ardo ya bayyana cewa lokacin da ya rage kafin zaben 2027 ya isa kwamitin kawancen siyasar ya yi rajista da kafa sabuwar jam’iyya, wacce za ta fito da kwarjini.
Don kare matsayinsu, Dr. Ardo ya jero wasu matsaloli da haɗarin da ke tattare da amfani da tsohuwar jam’iyya, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga manufar kawancen.
Shugaban kungiyar ya ce:
“Jam’iyyu irin su ADC da SDP sun riga sun kafa rassa a gundumomi, ƙananan hukumomi, jihohi da shiyyoyi, kuma shugabanninsu na kan karagar mulki bisa doka, kuma galibi ba sa son sauyi.
“Misali, shugaban ADC na Adamawa ya fito a fili ya ce wa’adin shugabancinsa da aka tabbatar masa a Zariya a Disambar 2022 zai kare ne a Disambar 2026, ka ga ba zai yarda a sauya shugabanci ba, dole a guje wa irin haka"

Source: Facebook
Tasirin sabuwar jam'iyyar hadakar 'yan adawa
LND ta ce amfani da irin wadannan jam’iyyu ba tare da daidaiton bukatu da iko ba, zai iya janyo rikici, rarrabuwar kawuna, shari’o’i da tabarbarewar tsari.
“A gefe guda kuma, kafa sabuwar jam’iyya na bayar da sabuwar dama ta akida, ingantaccen tsari, wanda zai iya jawo hankalin ‘yan Najeriya da suka gaji da tsofaffin jam’iyyu da alkawuran karya.”
- Dr. Ardo.
Dr. Ardo ya bukaci shugabannin kawancen da su hanzarta fara tsarin kafa sabuwar jam’iyya wadda za ta haɗa kan jama’a, kawo akida bayyananna da tsarin shugabanci mai inganci.
2027: Shekarau ya shiga hadakarsu Atiku
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, tare da wasu fitattun 'yan siyasar Arewa, sun shiga cikin yunkurin kafa hadakar 'yan adawa.
A wani taron kwamitin hadaka da aka gudanar a karshen Mayun 2025, kwamitin hadakar ya sanya ranar yanke hukunci kan jam’iyyar da za a yi amfani da ita.
Rotimi Amaechi ne ke jagorantar kwamitin da ke binciken yiwuwar kafa sabuwar jam’iyya, ko kuma a yi amfani da SDP ko ADC a matsayin jam'iyar hadaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


