Tun ba Ayi Zaben 2027 ba, An Fadi Yankin da Ya Kamata Shugaban Kasa Ya Fito a 2031

Tun ba Ayi Zaben 2027 ba, An Fadi Yankin da Ya Kamata Shugaban Kasa Ya Fito a 2031

  • Dr. Bashir Lamido na kungiyar Arewa Summit ya bukaci Kudu maso Yamma su fitar da ‘yan takarar shugaban kasa gaba daya a 2027
  • Ya ce a 2031, a ba Kudu maso Gabas cikakkiyar dama ta fitar da shugaban kasa, domin adalci da tabbatar da hadin kan Najeriya
  • Lamido ya ce Arewa ta fi jagorantar Najeriya a tarihi, don haka lokaci ya yi da za a daidaita shugabanci tsakanin yankuna bisa gaskiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kungiyar Arewa Summit, Dr. Bashir Lamido, ya bukaci yankin Kudu maso Yamma da ya fitar da dukkanin ‘yan takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Bayan zaben 2027, Dr. Bashir Lamido ya kuma nuna goyon bayansa a kan yankin Kudu maso Gabas ya samar da shugaban kasa a zaben 2031.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: An sanya ranar fara sabuwar zanga zangar adawa da mulkin Tinubu

Kungiyar Arewa Summit ta nemi yankin Kudu ya yi mulki daga 2027 har zuwa 2035
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da mataimakinsa, Kashim Shettima | Shugaban Arewa Summit, Dr. Bashir Lamido. Hoto: Sagacious Bello Lukman
Source: Facebook

An nemi Kudu maso Yamma su yi mulki a 2027

Dr. Lamido yayi wannan muhimmin kiran yayin wani taron tattaunawa kan tsarin karba-karba da hadin kan kasa da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar Arewa Summit ya jaddada cewa tsarin karba-karbar kujerar shugaban kasa tsakanin yankuna zai karfafa hadin kai, adalci da zaman lafiya a siyasar Najeriya.

“Domin adalci, hadin kai da dorewar dimokuradiyya, muna ganin ya dace Kudu maso Yamma su fito da dukkanin ‘yan takarar shugaban kasa a 2027.
“Daga nan kuma, a 2031, a ba yankin Kudu maso Gabas damar fito da dan takara, domin sun dade suna jiran wannan dama, kuma suna da manyan 'yan siyasar da za su iya yin shugabanci."

- Dr. Bashir Lamido.

Tasirin Arewa Summit ga siyasar Najeriya

Arewa Summit, karkashin jagorancin Dr. Lamido, ta kasance wata babbar kungiyar nazarin siyasa, wadda aka ce ta samu karbuwa a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

An ce kungiyar Arewa Summit na amfani da kwarewa da hangen nesa kan lamuran kasa baki daya da kuma jajircewa wajen gina hadin kai tsakanin yankuna.

Dr. Bashir Lamido ya kara jaddada cewa wannan tayin ba wai na ware wani yanki bane, sai dai tsari ne na kafa al’ada ta kasa da ta dace da gaskiya da hadin kai.

'A yi wa kowanne yanki adalci' - Dr Lamido

A cewar shugaban kungiyar Arewan:

“Ba wai siyasa kawai muke yi ba. Wannan magana ce ta samun waraka daga bangaranci, tare da gina amana da tabbatar wa kowanne dan Najeriya cewa yana da matsayi daya a wannan kasa.
“Wasu za su tambaya, ita kuma Arewa? Shin 2031 ba lokaci ne na shugabanci daga Arewa ba? Sun manta cewa Arewa ta fi kowanne yanki jagorantar kasar nan a tarihi.
“Ya dace mu daidaita shugabanci tsakanin yankuna. Muna fata a 2031, za a bai wa Kudu maso Gabas irin kyautatawar da muke fata a yi wa Kudu maso Yamma a 2027."
An nemi Kudu maso Yamma ta fito da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @officialABAT
Source: Facebook

'A jira Atiku ya fara shugabanci' - Surajo Caps

Kara karanta wannan

2027: Sanatoci sun gano dalilin kara karfin Boko Haram da sauran 'yan ta'adda

Yayin da yake zantawa da Legit Hausa kan wannan bukata ta Dr. Lamido, matashin dan siyasa daga Bauchi, Alhaji Surajo Caps, ya ce akwai bukatar a bari Atiku Abubakar ya fara mulki kafin a yi maganar kai takara Kudu.

A cewar Surajo Caps, jam'iyyar APC ta riga ta amince Shugaba Bola Tinubu ya yi tazarcen takara a 2027, don haka, Kudu ta samu tikiti a APC.

"Yanzu da ake maganar hadaka, muna da yakinin cewa duk jam'iyyar da za a yi amfani da ita domin hadakar za ta amince da Atiku Abubakar matsayin dan takararta.
"Idan hakan ta tabbata, ka ga kenan, muna da yakin Atiku ne zai yi nasara a 2027. To saboda dan Arewa ne sai ace idan ya ci zabe ba zai yi shugabanci ba, dole sai dan Kudu ne zai yi?
"Na yar da tsarin karba karba, to amma a bar wannan tsarin tukunna, domin siyasar 2027 za ta yi zafi fiye da tunani. Bayan 2027, to ko ma me za ayi sai a yi."

- Alhaji Surajo Caps.

Tsagin PDP zai ba dan Kudu tikiti a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu mambobin jam’iyyar PDP masu biyayya ga ministan Abuja, Nyesom Wike, sun fara shirye-shiryen janye goyon baya ga Atiku Abubakar a 2027.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Sanata ya halarci zaman majalisar dattawa sanye da rigar Tinubu

Bangaren Wike na PDP ya fara tattaunawa kan yiwuwar mara wa gwamnan Oyo, Seyi Makinde, baya a matsayin dan takara maimakon Atiku.

Bugu da ƙari, akwai tattaunawa kan yiwuwar komawar tsohon dan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi, zuwa PDP domin fuskantar zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com