"Lokaci Ya Yi da Zan Bar PDP," Gwamna Ya Ƙara Nuna Alamun Zai Koma APC kafin 2027

"Lokaci Ya Yi da Zan Bar PDP," Gwamna Ya Ƙara Nuna Alamun Zai Koma APC kafin 2027

  • Gwamnan jihar Akwa Ibom ya kara tabbatar da shirinsa na sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Fasto Umo Eno ya ce har yanzu yana kaunar PDP, amma dai lokaci ya yi da ya kamata ya matsa zuwa mataki na gaba
  • Gwamna Eno ya yi wannan furuci ne a wurin liyafa ta musamman da aka shirya domin bikin cikarsa shekara biyu a kan gadon mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya sake nuna alamar cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP.

Gwamna Eno ya bayyana lamar cewa zai sauya sheka daga PDP zuwa APC duk da dai bai ambaci sunan jam'iyyar da zai koma ƙarara ba.

Gwamna Umo Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya kara nuna alamar zai sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

Gwamna Eno ya nuna alamar barin PDP

Kara karanta wannan

"Zan ga masu ƙaunata na gaskiya," Gwamna ya bayyana shirinsa na komawa APC

Da yake jawabi a wurin wata liyafa da aka shirya a Uyo, Gwamma Eno ya jaddada cewa yana matuƙar kaunar PDP amma lokaci ya yi da zai barta, in ji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya liyafa ta musamman da daddare ranar Alhamis domin bikin cikar gwamnan shekaru biyu a kan mulki.

Gwamna Eno ya sake jaddada kaunarsa ga PDP, amma ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da zai “cigaba da tafiya a hankali zuwa matakin ci gaba.”

“Ina girmama jam’iyyarmu, PDP. Ina ƙaunar PDP amma kowa ya san yadda abubuwa suke tafiya.
"Don haka, duk abin da ya faru, duk inda tafiyar rayuwa ta kai ni, zan ci gaba da ƙaunarku. Mun gina kyakkyawar zumunta, kuma za mu ci gaba da kareta.”

- Umo Eno.

Wace jam'iyya Gwamna Umo Eno zai koma?

Tun da aka fara raɗe-raɗin sauya shekarsa, Gwamna Eno ya riƙa kaucewa ambatar APC kai tsaye, duk da ya fito ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.

A rahoton Premium Times, Gwamna Eno ya ƙara da cewa:

"Idan kuna da wani taro ko wani abu da kuka shirya za ku yi, ku gayyace ni, zan zo. Zan kasance tare da ku a kullum. Amma lokaci ya yi da zan motsa zuwa matakin ci gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fara shan yabo da ya ba shugaban APC kyautar danƙareriyar mota

"Wannan ba zai shafi komai a jiharmu ba. Ba siyasa ce ke jagorantar yadda muke mulki ba.”
Gwamna Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya tabbatar wa ƴan PDP cewa yana nan tare da su ko da kuwa ya sauya sheƙa Hoto: Pastor Umo Eno
Source: Facebook

Gwamna ya jaddada bukatar haɗa kai

Yayin da yake kira ga haɗin kai tsakanin shugabannin siyasa, Umo Eno ya ƙara da cewa:

"Ina son ganin dukkan shugabannin jam’iyyunmu na zaune tare kamar haka, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
"Dole ne mu sanya Akwa Ibom a gaba. Mun san akwai ‘yan Akwa Ibom a cikin PDP, APC, YPP, da IPAC.
"Abin da ya fi muhimmanci shi ne mu tabbatar da wadatar abinci, tsaro da jin daɗin jama’a. Ajendar da na ɓullo da ita watau ARISE tana samar da duk waɗannan abubuwan.”

"APC da PDP duk manufarsu 1"- Gwamna Eno

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno ya yi ikirarin cewa duka jam'iyyun siyasa manufarsu ɗaya, babu wani abu da ya banbanta su face suna.

Gwamna Eno, wanda alamu suka tabbatar da yana shirin sauya sheka, ya yi ikirarin cewa da APC da PDP duk abu guda ne domin manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.

Ya kwatanta jam'iyyun siyasa da tsani wanda ake takawa domin a ci zaɓe amma bayan mutum ya yi nasara, zai zama shugaba ga kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262