Tsohon Shugaban PDP Ya Kawo Mafita, Ya Faɗi Gwamnan da Ya Dace da Mulkin Najeriya a 2027
- Ana ci gaba da kiraye-kiraye ga gwamnan Oyo, Seyi Makinde domin ya fito takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP a zaɓen 2027
- Tsohon shugaban PDP a Oyo kuma hadimin gwamnan, Kunmi Mustapha ya buƙaci Makinde ya fara shirin neman mulkin Najeriya
- Ya ce Gwamnan ya kawo ci gaba a Oyo a tsawon shekaru shida da ya yi a kujerar mulki don haka ake masa babban hange a a zaɓe mai zuwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Oyo, Kunmi Mustapha, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Seyi Makinde a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2027.
Mustapha ya buƙaci Gwamna Makinde ya fara shirye-shiryen neman kujera lamba ɗaya a ƙasar nan domin yana da duk abin da ake buƙata wajen ceto Najeriya.

Source: Twitter
Tsohon shugaban PDP ya faɗi haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Ibadan ranar Alhamis domin taya gwamna Makinde murnar cika shekaru shida a kan mulki, Tribune Nigeria ta rahoto.
'Gwamna Makinde ya cancanci zama shugaban ƙasa'
Mustapha ya yaba da kwarewar shugabanci da jajircewar Makinde, yana mai cewa shi ya fi cancanta ya jagoranci Najeriya idan aka yi la’akari da ayyukan da ya yi a Oyo.
“Halin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ba yana nufin cewa ba za ta iya kwace mulkin ƙasa ba a 2027,” in ji shi.
Ya ce nasarorin da Makinde ya samu a jihar Oyo hujja ce ta cancantarsa a matakin kasa, yana mai jaddada cewa:
"Gagarumin ci gaban da ya kawo a jihar Oyo, da gudunmuwarsa ga ci gaban Najeriya, ba su da kishiya.”
Wace mafita tsohon shugaban PDP ya kawo?
Mustapha ya bukaci ‘yan Najeriya su mara wa ‘yan siyasar da ke nuna damuwa da jin daɗin jama’a baya, maimakon waɗanda ke haifar musu da wahala.

Kara karanta wannan
Ondo: Ɗan Majalisar Tarayya 1 tilo da PDP ke taƙama da shi ya sauya sheƙa zuwa APC
“Makinde mutum ne mai jarumtaka da kwarewar shugabanci ta musamman. Ban ga wani ɗan siyasa a yankin Yarbawa da ya ke da hangen nesa na ci gaban talakawa irinsa ba.
"Sai dai marigayi Pa Obafemi Awolowo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ganin an cimma wannan buri.”
Nasaarorin Gwamna Makinde a Oyo
Ya bayyana cewa tun da ya zama gwamna a 2015, Makinde ya samu nasarori a fannoni da dama kamar, ilimi, lafiya, noma, ayyukan raya kasa da walwalar jama'a.
A rahoton Punch, jigon PDP ya ci gaba da cewa:
“Tun daga gyaran birane, inganta ilimi, lafiya da gine-ginen muhimman abubuwa, har zuwa tallafa wa harkar noma da walwalar ma’aikata, da kuma bai wa matasa da tsofaffi dama, Gwamna Makinde ya nuna ba shi da tsara.”

Source: Facebook
Kunmi Mustapha, wanda yanzu haka ke aiki a matsayin mai ba gwamnan shawara kan harkokin siyasa, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga duk wata manufa ta siyasa da Makinde zai ɗauka nan gaba.
“Komai tsanani, muna tare da shi. Don haka muna roƙon ya fara shiri tun yanzu domin tunkarar 2027.”
Ya kuma yaba wa wasu manyan jagororin PDP irin su muƙaddashin shugaban jam'iyya na kasa, Umar Damagum, da mataimakinsa na Kudu, Taofeek Arapaja.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027
Fastocin kamfen Makinde sun shiga Kano
A wani labarin, kun ji cewa fastocin takarar shugaban ƙasar Gwamna Makinde sun mamaye muhimman wurare a kwaryar birnin Kano.
An ga fastocin a wuraren da jama’a ke hada-hada kamar kewayen filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA), yankin Wapa da gadar Dangi.
Matasan da suka liƙa fastocin sun ce wannan somin taɓi ne domin nan ba da jimawa za a ga allunan kamfen Makinde a mafi yawan jihohin Arewa.
Asali: Legit.ng
