Shekara 2 a Mulki: Fadar Shugaban Kasa Ta Kausasa Harshe ga Atiku kan Sukar Tinubu

Shekara 2 a Mulki: Fadar Shugaban Kasa Ta Kausasa Harshe ga Atiku kan Sukar Tinubu

  • Mai bai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya caccaki Atiku Abubakar kan sukar da yayi wa Bola Tinubu
  • Onanuga ya bayyana cewa Atiku na nuna kiyayya ce kawai ba tare da la'akari da nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu ba
  • Ya lissafa wasu daga cikin muhimman sauye-sauyen tattalin arziki da manufofin da gwamnatin ta aiwatar cikin shekaru biyu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya yi martani ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kan kalaman da ya yi na sukar Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 29 ga Mayu, 2025, Onanuga ya ce Atiku na rura wutar adawa ne da gangan ba tare da duba hakikanin nasarorin da aka samu cikin shekaru biyu ba.

Kara karanta wannan

'Mutum sama da 10,000 aka yiwa kisan gilla a mulkin Tinubu," Amnesty Int'l

Fadar shugagan kasa
Fadar shugaban kasa ta caccaki Atiku kan sukar Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar
Source: Twitter

Legit ta gano cewa Bayo Onanuga ya yi wa Atiku Abubakar martani ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce ya kamata Atiku ya yaba da irin sauye-sauyen da gwamnatin ta kawo, musamman wadanda shi da Obasanjo suka kasa aiwatar a shekarun da suka wuce.

Fadar shugaban kasa ta yi wa Atiku martani

Bayo Onanuga ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da mafi kyawun gyaran tattalin arziki da tsarin gwamnati cikin shekara biyu.

Ya ce cire tallafin fetur da daidaita tsarin musayar kudi matakan gyara ne da sauran gwamnati suka kasa dauka.

A cewarsa, ko da kuwa matakan suna da radadi, sun taimaka wajen daidaita kasafin kudin kasa, rage cin hanci, da kuma kara janyo masu zuba jari daga kasashen waje.

Onanuga ya ce Tinubu ya tallafawa talakawa

Onanuga ya bayyana cewa gwamnati ta fahimci irin tasirin da matakan gyaran tattalin arzikin ke yi wa masu karamin karfi, dalilin da ya sa ta kirkiro da hanyoyin tallafa wa jama'a.

Kara karanta wannan

2027: Sanatoci sun gano dalilin kara karfin Boko Haram da sauran 'yan ta'adda

Ya ce an kara albashi daga N30,000 zuwa N70,000, wasu jihohi ma suna biyan har N85,000. Haka kuma, an kaddamar da tsarin bashin karatu ga dalibai domin rage cikas a fannin ilimi.

Onanuga
Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu ya yi kokari a shekara 2. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Onanuga ya zargi Atiku da wuce gona da iri

Mai bai wa shugaban kasa shawara ya ce Atiku ya nuna rashin adalci wajen sukar gwamnatin Tinubu, inda ya ke watsi da nasarorin da aka samu a fannin kudi da farfado da tattalin arziki.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta biya bashin IMF na $3.4bn da aka ci lokacin annobar COVID-19.

Bayo Onanuga ya yi kira ga Atiku

A karshe, Onanuga ya bukaci Atiku da sauran ‘yan adawa su dinga gabatar da ingantattun mafita a maimakon sukar gwamnati ba tare da bayar da madogara ba.

Ya ce gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da mutunta ‘yancin ‘yan Najeriya na sukar gwamnati, amma ana bukatar adawa wacce ke haifar da mafita, ba kawai surutu da fushi ba.

Bayo Onanuga ya bukaci 'yan Najeriya su yi wa gwamnati adalci wajen lura da ayyukan da ta yi ba wai lura da magananganun irinsu Atiku da suka yi watsi da damar da suka samu a baya ba.

Kara karanta wannan

Atiku ya tono manyan 'kurakuran' Tinubu a shekara 2, ya yi raddi mai zafi

Atiku ya ce Tinubu ya kawo talauci Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta kara talauci a Najeriya.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne yayin da Bola Tinubu ya cika shekara biyu a kan madafun iko a Najeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce 'yan adawa za su cigaba da kokarin samar da mafita ga Najeriya, musamman a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng