Gwamna Zai San Makomarsa a Yau, da Yiwuwar Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tsige Shi

Gwamna Zai San Makomarsa a Yau, da Yiwuwar Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tsige Shi

  • A yau Alhamis, 29 ga watan Mayu, 2025, kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci a karar da aka kalubalanci nasarar gwamnan Edo, Monday Okpebholo
  • Jam'iyyar PDP da ɗan takararta, Asue Ighodalo ne suka shigar da ƙarar, inda suka ce an tafka kura-kurai a zaɓen 21 ga watan Satumba, 2024
  • Kotun sauraron kararrakin zaɓe ta tabbatar da nasarar Gwamna Okpebholo a hukuncin da ta yanke ranar 2 ga watan Afrilu, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta shirya yanke hukunci a yau Alhamis kan karar da ke kalubalantar sakamakon zaben gwamnan jihar Edo.

Idan ba ku manta ba, Gwamna Monday Okpebholo na jam’iyyar APC ne ya lashen zaɓen gwamnan Edo da aka yi ranar 21 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027

Gwamna Okpebholo da Asue Ighodalo.
Kotun ɗaukaka ƙara za ta yanke hukunci kan ƙarar zaben gwamnan jihar Edo a yau Hoto: Asue Ighodalo, Monday Okpebholo
Source: Twitter

Edo: Kotun ɗaukaka ƙara za ta yi hukunci yau

Kwamitin alkalai uku ne zai yanke hukunci a ƙarar da aka ɗaukaka zuwa gaban kotun, wadda aka nemi tsige Gwamna Okpebholo, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran kotun za ta tantance ko ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan ta yanke a ranar 2 ga Afrilu ko kuma a soke shi.

Jam'iyyar PDP da ɗan takararta na gwamna, Asue Ighodalo ne suka ɗaukaka ƙara suna kalubalantar hukuncin kotun zaɓe, wacce ta tabbatar da nasarar APC a zaɓen Edo.

PDP da Ighodalo sun ɗaukaka ƙara a kotu

Mr. Ighodalo da PDP sun kalubalanci hukuncin kotun zabe da ta yi watsi da karar da suka shigar kan sakamakon da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta sanar.

INEC ta ayyana Mr. Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 291,667, yayin da Mr. Ighodalo ya zo na biyu da kuri'u 247,655.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya fara shan yabo da ya ba shugaban APC kyautar danƙareriyar mota

Wasu 'yan takara da dama sun shiga zaben, amma sun samu kashi kadan na kuri'un da aka kada.

Sai dai Mr. Ighodalo ya tafi gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Edo da ke zama a Abuja, inda ya kalubalanci sakamakon zaben

Ya shaida wa kotun cewa an samu kura-kurai da magudi, da kuma rashin bin dokar zabe yadda ya kamata a zaɓen watan Satumba, 2024, Daily Post ta rahoto.

Gwamnan Edo da ɗan takarar PDP.
Gwamna Okpebholo ya kalubalanci wasu ɓangarori a hukuncin kotun zaɓe Hoto: @M_Akpakomiza, Asue Ighodalo
Source: Facebook

Wane hukunci kotun zaɓe ta yanke?

Kotun zaɓe, a hukuncinta na watan Afrilu ta yi watsi da karar, tana mai cewa hujjojin da masu kara suka gabatar ba su gamsar ba.

Duk da hakan, Mr. Ighodalo ya dage kan cewa karar tasa na da tushe, don haka ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara.

A bangare guda, duk da Gwamna Okpebholo ne ya samu nasara a kotun zaɓe, shi ma ya ɗaukaka ƙara yana mai ƙalubalantar wasu ɓangarorin hukuncin da aka yanke.

Kowane hukunci kotun daukaka kara ta yanke a yau, ba zai zama na karshe ba, domin har yanzu ɓangarorin na da damar ɗaukaka kara zuwa kotun koli.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun shari'a ta yi hukunci, za a kashe matashin da ya babbake masallata

Jam'iyyar APC ta ƙara karfi a jihar Edo

A wani labarin, kun ji cewa kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo, Rt. Hon. Blessing Agbebaku ya jagoranci ciyamomin kananan hukumomi 17 sun fice daga PDP zuwa APC.

Kakakin majalisar ya ce sun dauki wannan matakin ne domin haɗa kai da Gwamna Monday Okpebholo wajen kawo ci gaba a Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262