"Kuɗin Kamfe," Ɗan Atiku Ya Tayar da Ƙura, Ya Jero Abubuwa 3 da Tinubu Zai Yi da Bashin N40trn
- Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya caccaki yunkurin gwamnatin Bola Tinubu na runtumo bashin Naira tiriliyan 40
- Shehu Atiku Abubakar ya yi zargin cewa Tinubu zai karɓo bashin ne domin kamfe, cike giɓin kasafi da ba bayyana ba da titin gaɓar teku
- Ya kuma koka kan cire tallafin wuta, fetur da ilimi, yana mai cewa gwamnatin ba ta damu da talakawa ba face masu arziki da ƙarfin iko
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Adamawa - Shehu Atiku Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi tsokaci kan sabon bashin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ke shirin karɓowa.
Shehu Atiku ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke shirin sake runtumo wa Najeriya rancen kuɗi har Naira triliyan 40.

Source: Twitter
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 27 ga watan Mayu, 2025, ɗan Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da karɓo wannan rance saboda kamfen 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu zai runtumo wa Najeriya bashi
A ganinsa, Shugaba Tinubu ya tuge tallafin man fetur, tallafin wutar lantarki da na ilimi, amma yanzu ya dawo zai runtumo bashi don kamfe da cike giɓin kasafin da ba a bayyana ba.
Idan ba ku manta ba Tinubu ya aika da wasiƙa zuwa Majalisar Wakilai yana neman amincewa da shirin neman bashi na $21.5bn daga ƙasashen waje.
Haka nan kuma, ya buƙaci izinin samun rance daga cikin gida na N757.9bn domin biyan bashin fanshon da ma'aikata ke bin da gwamnati.
Ɗan Atiku ya tayar da kura kan shirin Tinubu
Da yake martani, Shehu Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da shirin karɓo bashin Naira tiriliyna 40 domin abubuwa uku, da suka haɗa da:

Kara karanta wannan
Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207
1. Kuɗin yakin neman zaɓe
2. Kudin cike gibin kasafin kuɗin da ba a bayyana ba
3. Naira tiriliyan 15 don gina titin gaɓar teku na kamfanin Oga.

Source: Twitter
Bayan haka, ɗan tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma jero abubuwa uku da Tinubu ya cire kuɗinsu duk da amfaninsu ga talaka;
1. Tallafin wutar lantarki
2. Tallafin man fetur
3. Tallafin ilimi.
"Gwamnatin masu ƙarfi da mulki, daga masu mulki kuma domin masu mulki," in ji shi.
Mutane sun maidawa Shehu Atiku martani
Wannan zargi na ɗan Atiku ya ja hankalin jama'a, inda mutane suka fara masa martani, wasu na goyon bayansa, wasu kuma na ganin siyasa ce kawai.
Osaro PhD ya ce:
"Ka faɗi gaskiya a nan, za su runtumo wannan bashin ne domin su sayi ƙuri'u a 2027."
Auwvl80 ya ce:
"Sun cire tallafin mai ne don kauce wa ɗauko bashi, amma yanzu suna neman bashi fiye da na da. To me ya faru da cire tallafi kenan?"

Kara karanta wannan
Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027
Abdul'azeez Salaudeen ya ce:
"Mahaifinka ya yi amfani da kuɗin ’yan Najeriya ya gina jami’arsa alhali dalibai na yajin aiki fiye da shekara guda a wancan lokacin, Allah zai yi masa hisabi."
Atiku ya gana da El-Rufai a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya ziyarci Malam Nasir El-Rufai a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.
Atiku ya samu rakiyar Dujiman Adamawa, Alhaji Musa Halilu Ahmed zuwa gidan tsohon gwamnan na Kaduna, kuma sun tattauna batutuwa da dama.
Ana ginin cewa El-Rufa’i da Atiku Abubakar na ƙara kusantar juna bayan sauya shekar El-Rufa’i zuwa jam’iyyar SDP.
Asali: Legit.ng
