"Ba Zai Yi Nasara ba": Fitaccen Malami Ya Hango Abin da Zai Faru a Zaben 2027

"Ba Zai Yi Nasara ba": Fitaccen Malami Ya Hango Abin da Zai Faru a Zaben 2027

  • Fitaccen fasto, Major Prophet, ya yi hasashen cewa za a fara sayen limamai da shugabannin addini daga 2025 don su mara wa ’yan siyasa baya
  • Ya gargadi cewa majami’u za su zama wuraren kamfen, inda fastoci da bishof za su yi goyon bayan ’yan takara saboda kudi da alfanun kashin kai
  • Major Prophet ya ce duk dan siyasa da ya dogara da goyon bayan fastoci ba zai yi nasara ba; wannan dabi’a za ta taimaka wa ’yan adawa ne kawai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Fitaccen fasto, Major Prophet, ya yi gargadi cewa kafin babban zaben 2027, ’yan siyasa za su yi kokarin sayen malamai da shugabannin addini.

Ya yi hasashen cewa za a samu malamai da dama da za su fada tarkon 'yan siyasa, inda za su bayyana goyon bayansu ga wasu jam’iyyun siyasa saboda kudi ko wasu bukatu na duniya.

Kara karanta wannan

'Mata masu sanya sarkar kafa karuwai ne': Fasto ya ba da sabuwar fatawa

Fasto Major Prophet ya ce 'yan siyasa za su saye malaman addini a 2027, kuma za su fadi zabe
Major Prophet ya fadi makomar 'yan siyasar da za su sayi malaman addini a 2027. Hoto: @officialABAT, @PeterObi
Source: Twitter

Malamin addini ya magantu kan zaben 2027

Legit Hausa ta ci karo da bidiyon wannan fitaccen malamin ne a shafin Possibility TV da ke manhajar YouTube, inda Major Prophet ya tabo batutuwa da dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Major Prophet ya ce duk wani dan siyasa da ya kudurta amfani da malamai a yakin neman zabensa, ba zai yi nasara ba, abokin hamayyarsa ne zai lashe zaben.

Ya yi ikirarin cewa, 'yan siyasa za su fara tuntubar manyan malamai da shugabannin addini tun daga shekarar 2025, kuma za su yi masu tayin kudi.

'Coci za su zama wurin yakin neman zabe' - Fasto

A cewar hasashensa, jam’iyyun siyasa za su fara janyo shugabannin addinai da nufin amfani da wuraren ibadarsu a matsayin matakin samun goyon baya daga jama’a.

Major Prophet ya bayyana yadda limamai da bishof-bishof za su fara fitowa fili suna goyon bayan ’yan takara, galibi saboda abin hannun 'yan siyasar.

Kara karanta wannan

Kano: Fusatattun matasa sun cinnawa ofishin ƴan sanda wuta, an ji abin da ya faru

Ya ce:

“Na ga wani abu a cikin duniyar siyasa. Na ga yadda za a fara cinikayya da majami'u. Za a fara sayen fastoci domin su mara wa jam’iyyun siyasa baya.
“Za ku ga bishof suna rike makirufo suna tallata ’yan takara. Za a fara sayen imanin fastoci da majami'unsu daga shekarar 2025.”
“A daina kawo ’yan siyasa dakin ibada don yakin neman zabe. Sakamakon hakan shi ne, mafi yawan ’yan takarar da suka sayi fastoci, ko da shugaban kasa ne, ba za su ci zabe ba. Wannan dabi’a za ta taimaka wa ’yan adawa ne kawai.”

Damuwar jama'a kan cusa siyasa cikin addini

Wannan hasashe ya haifar da cece-kuce a cikin al’umma, inda mutane ke nuna damuwa kan yadda ake kokarin cakuda addini da harkokin siyasa.

Yayin da Najeriya ke kara kusantar zaben 2027, mutane za su ci gaba da sanya idanu domin ganin ko wannan hasashe na Major Prophet zai tabbata, inji rahoton Legit.ng.

Kara karanta wannan

Makiyaya dauke da makamai sun harbe malamin addini a Makurdi, sun sace mutane 2

Ko hakan zai faru ko a’a, wannan gargadi ya riga ya bude sabon babin tattaunawa kan rawar da addini ke takawa wajen sauya sakamakon zabuka.

Fasto ya ce 'yan siyasa za su saye shugabanni da malaman addini gabanin 2027
Fasto Major Prophet ya ce 'yan siyasa za su mayar da coci wajen yakin neman zabe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ra’ayoyin jama’a kan hasashen Major Prophet

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a dangane da hasashen na Major Prophet:

@temitopeawe1034:

"Ba na zargin ’yan siyasa. Matsalar tana wajen shugabannin coci. Gaskiya muna dogaro da malamai fiye da kima, muna ajiye duk wani tunani namu idan mun shiga cikin coci."

@Bobohappyguy:

"Peter Obi ba zai ci zaben 2027 ba, wannan shi ne hasashen kawai."

@michaelefedi9338:

"Tabbas Tinubu ba zai ci zaben 2027 ba."

Kalli bidiyon a nan kasa:

'Abin da zai faru da APC a 2027'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ana cigaba da tattaunawa kan yadda zaɓen shugaban ƙasa na 2027 zai kasance a Najeriya.

Jigo a jam’iyyar PDP kuma shugaban tafiyar, Segun Sowunmi, ya yi hasashe game da makomar APC a zaɓen mai zuwa.

A cewarsa, jam’iyyar APC za ta fuskanci abin mamaki a zaɓen, la’akari da yadda take nuna isa da cika baki a harkokin siyasar ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com