APC Ta Kara Raunata PDP, LP a Majalisa, yayin da Mambobinsu Suka Koma Jam'iyyar
- Jam'iyyun adawa na PDP, LP sun samu naƙasu a majalisar wakilan Najeriya bayan wasu mambobinsu sun fice zuwa APC
- Ƴan majalisun sun bayyana dalilan da suka sanya suka fice daga jam'iyyunsu zuwa jam'iyya mai mulki a Najeriya
- Sauya sheƙar ta su ta sanya rinjayen da jam'iyyar APC take da shi ya ƙaru a majalisar wakilan Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta ƙara samun tagomashi a majalisar wakilai.
Mambobi biyu na jam'iyyun PDP da LP, Okolie Lawrence da Akingbaso Olanrewaju, sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Jaridar TheCable ta ce shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya sheƙar tasu a zaman majalisar na ranar Laraba, 28 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisa sun sauya sheƙa daga hamayya
Majalisar wakilai ta 10 ta sha samun sauyin sheƙa daga mambobinta tun bayan kafuwarta.

Kara karanta wannan
Ondo: Ɗan Majalisar Tarayya 1 tilo da PDP ke taƙama da shi ya sauya sheƙa zuwa APC
A ranar 2 ga watan Oktoba, 2024, Chris Nkwonta, mai wakiltar mazaɓar Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma a jihar Abia, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC.
A ranar 30 ga watan Oktoba kuma, Sulaiman Abubakar daga Gummi/Bukkuyum a jihar Zamfara, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki.
Har zuwa ranar 5 ga watan Disamba, mambobi huɗu daga jam’iyyar LP da ɗaya daga PDP sun koma APC, wanda hakan ya ƙara yawan mambobin APC a majalisar.
Al’amarin ya ci gaba da gudana a ranakun 11 da 12 ga Fabrairu, inda Amos Magaji daga jihar Kaduna da Garba Koko daga jihar Kebbi suka bar PDP suka shiga APC.
Meyasa ƴan majalisar PDP, LP suka koma APC?
Okolie Lawrence, wanda ke wakiltar mazaɓar Aniocha ta Arewa/Aniocha ta Kudu/Oshimili ta Arewa/Oshimili ta Kudu a jihar Delta, ya kasance ɗan jam’iyyar LP.
Ya bayyana cewa sauya sheƙarsa zuwa APC zai kawo mulki kusa da al’ummar mazaɓarsa.
Akingbaso Olanrewaju, tsohon ɗan jam'iyyar PDP, wanda ke wakiltar mazaɓar Idanre/Ifedore a jihar Ondo, ya ce rikicin cikin gida da jam’iyyar PDP ke fama da shi ne ya sa ya yanke shawarar komawa APC, cewar rahoton The Nation.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa yana so ne ya daidaita kansa da akidar APC da kuma shirin ‘Renewed Hope’ na Shugaba Bola Tinubu.
Sauya shekar Olanrewaju ya haifar da ƙorafi daga shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, wanda ya yi magama yana mai cewa babu wani rikici da ke cikin PDP.
Shugaban majalisar ya amince da ƙorafin, amma ya ci gaba da gudanar da ayyukan yau na majalisar.
PDP ta kai ɗan majalisa ƙara kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta maka ɗan majalisar wakilai daga jihar Osun, Olusola Oke, a gaban kotu.
PDP ta kai ɗan majalisar ƙara ne a gaban kotu tana neman tuɓe shi daga kujerarsa kan komawa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.
Lauyan jam’iyyar reshen Osun, Raphael Oyewole, ne ya shigar da ƙarar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a madadin PDP.
Asali: Legit.ng
