NEC: Atiku, Wike da wasu Jiga Jigan PDP Sun Yi Watsi da Babban Taron Jam'iyya

NEC: Atiku, Wike da wasu Jiga Jigan PDP Sun Yi Watsi da Babban Taron Jam'iyya

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike sun ki halartar taron kwamitin zartarwa na PDP
  • Baya ga Atiku da Wike, tsofaffin shugabannin majalisa; David Mark da Aminu Tambuwal sun yi watsi da taron da aka gudanar a ranar Talata
  • Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Prince Diran Odeyemi ya bayyana cewa rashin halartar manyan ba ya nufin matsala ce

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike sun kauracewa taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar.

A cewar rahotannin, shugabannin biyu sun ci gaba da nesanta kansu daga harkokin jam’iyyar, duk da cewa an samu yunkurin wasu na kawo sulhu a rikicin PDP da ya ki ci, ya ki cinyewa.

Kara karanta wannan

Hadaka: Atiku ya ziyarci El Rufa'i, sun tattauna makomar Najeriya

Atiku
Atiku da Wike ba su halarci taron NEC na PDP ba Hoto: Atiku Abubakar/Nyesom Wike
Source: Facebook

The Guardian ta wallafa cewa duk da taron ya gudana kamar yadda aka tsara, an samu rashin halartar wasu daga cikin jiga-jigan PDP da suka yi watsi da zaman.

Jiga-jigan PDP sun kauracewa taron

TVC News ta bayyana cewa baya ga Atiku da Wike, wasu fitattun ‘yan jam’iyyar kamar tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon shugaban majalisar wakilai, Aminu Tambuwal ba su je taron ba.

Sai dai tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Prince Diran Odeyemi, ya bayyana cewa rashin zuwansu ba ya nufin sun fice daga jam’iyyar ko suna adawa da tafiyar.

A cewarsa:

“Mu bar batun yadda yake, rashin zuwansu jiya (Talata) ba yana nufin ba za a gan su yau ba.”

Ya kara da cewa bai dace a rika fassara rashin halartar manyan jam'iyyar ba, duk da an samu rade-radin wasu na iya barin jam'iyyar saboda hadakar adawa.

PDP ta fitar da matsaya bayan taro

Kara karanta wannan

Hasashen El Rufai ya tabbata, SDP mai kokarin kwace mulki ta shiga Matsala

Bayan kammala taron NEC, mukaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Damagum, ya karanta wata sanarwa dauke da shawarwari 10 da suka cimma.

Damagum
Shugaban PDP ya fadi matsayar da aka cimma bayan taron NEC Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

An bayyana Gwamna Douye Diri a matsayin shugaban kwamitin rabon mukamai, yayin da Gwamnoni, Dauda Lawal da Caleb Mutfwang ke matsayin mataimaki da sakatare.

Haka zalika, an kafa kwamitin shirya babban taron jam’iyya na ƙasa, tare da Gwamna Ahmadu Fintiri a matsayin shugaban kwamitin, Ademola Adeleke a matsayin mataimaki, da Peter Mbah a matsayin sakatare.

PDP: ‘Tinubu na tsoron faduwa zabe'

A baya, kun ji cewa PDP ta sake jaddada zargin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC na ƙulla shiri na maida Najeriya karkashin tsarin jam’iyya ɗaya saboda son kai.

Shugaban rikon kwarya na PDP na ƙasa, Ambasada Umar Iliya Damagum, ya bayyana cewa wannan yunƙuri na kara ƙarfi ne saboda tsoron da Tinubu ke ji na fuskantar matsala a zaɓen 2027.

Ambasada Damagum ya ce PDP ba za ta yi shiru ba yayin da ake yunƙurin murkushe dimokuraɗiyya a ƙasar, yana mai kiran ‘yan Najeriya da su tashi tsaye su kare ƙasarsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng