PDP Ta Taso Tinubu a Gaba, Ta Fadi Babban Tsoronsa a Zaben 2027

PDP Ta Taso Tinubu a Gaba, Ta Fadi Babban Tsoronsa a Zaben 2027

  • Jam'iyyar PDP mai adawa ta gudanar da taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) a babban birnin tarayya Abuja
  • Bayan kammala taron PDP ta zargi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da yunƙurin maida Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya
  • PDP ta nuna cewa Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC na yin wannan yunƙurin ne don tsoron samun rashin nasara a zaɓen shekarar 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC da ƙulla makircin mayar da Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya.

PDP ta bayyana cewa wannan yunƙuri na faruwa ne saboda tsoron da Shugaba Tinubu ke ji na fuskantar rashin nasara a zaɓen 2027.

PDP ta zargi Bola Tinubu
PDP ta zargi Tinubu da yunkurin maida Najeriya karkashin jam'iyya 1 Hoto: @OfficialPDPNig, @OfficialABAT
Source: Twitter

Matsayar jam’iyyar ta fito ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X a ranar Talata, bayan taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Shugaban PDP ya bayyana matakin dauka kan masu haddasa rikici a jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar na ɗauke da sa hannun muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum.

Jam'iyyun adawa na cikin rikici a Najeriya

Jam’iyyu masu hamayya da suka haɗa da PDP, LP da NNPP sun fuskanci yawaitar ficewar mambobinsu a cikin makonnin da suka gabata.

Wannan ci gaba ya jawo cece-kuce daga masu ruwa da tsaki daban-daban, waɗanda ke ganin cewa gwamnatin APC na ƙoƙarin tura Najeriya cikin tsarin siyasar jam’iyya ɗaya.

PDP ta zargi Tinubu da yunƙurin murƙushe adawa

Sai dai babbar jam’iyyar adawar ta bayyana tsayuwarta kyam wajen ƙin yarda da wannan shiri da shugaban ƙasa da jam’iyyarsa ke ƙullawa.

Umar Damagum
PDP ta ce Tinubu na tsoron faduwa a zaben 2027 Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter
“NEC na nuna tsayuwarta kai-da-fata wajen ƙin amincewa da wannan mummunan makirci da jam’iyyar APC ƙarƙashin shugabancin Tinubu ke yi na mayar da Najeriya ƙarƙashin jam'iyya ɗaya da ƙarfi da yaji."
"Hakan a bayyane yake yadda ake iya gani a ƙoƙarinsu na kakkaɓe jam’iyyun adawa ta hanyar mamaya kai tsaye, barazana da tsoratarwa ga shugabannin adawa da kuma cibiyoyin dimokuraɗiyya a ƙasar nan.”

Kara karanta wannan

"Ba za ta sabu ba": Gwamnonin PDP sun nuna yatsa ga gwamnatin tarayya

"A bayyane yake cewa wannan shiri ya samo asali ne daga matsanancin tsoron APC na fuskantar tabbatacciyar rashin nasara a 2027 sakamakon gazawarsu a mulki.”
“A ɓangaren PDP, NEC na sake jaddada cewa jam’iyyarmu na da cikakken amanna kan dimokuraɗiyya, bin doka da oda, da kuma fifikon ra’ayin jama’a kamar yadda yake ta hanyar shiga harkokin zaɓe da mulki cikin yanayin jam’iyyu da dama ba tare da tsangwama ba."

- Umar Damagum

Ƴan PDP sun koma APC a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu manyan siyasa na jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a jihar Sokoto.

Ƴan siyasan sun samu tarba daga wajen Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko wanda ya nuna jindaɗinsa kan matakin da suka ɗauka.

Sun bayyana cewa sun shigo jam'iyyar PDP ne don ba da irin ta su gudunmawar wajen ci gaban jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng