Zaben 2027: 'Yan Majalisa Sun Yi Matsaya kan Tazarcen Gwamna Radda
- Gwamna Dikko Radda ya samu tagomashi idan ya ƙuduri aniyar neman tazarce a zaɓen shekarar 2027
- Ƴan majalisar dokokin jihar sun amince gwamnan ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC
- Sun bayyana cewa sun gamsu da salon mulkin Gwamna Radda da kuma irin ci gaban da ya kawo a jihar Katsina
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan majalisar dokokin jihar Katsina sun bayyana matsayarsu kan tazarcen Gwamna Dikko Radda a zaɓen 2027.
Ƴan majalisar dokokin sun amince da goyon bayan Gwamna Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara karo na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Source: Facebook
Shugaban majalisar dokokin, Nasiru Yahaya mai wakiltar mazaɓar Daura wanda ya yi jawabi a madadin sauran ƴan majalisar ya sanar da amincewar yayin wani taron manema labarai, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan amincewa ta zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan ƴan majalisar tarayya daga jihar, ƙarƙashin jagorancin Sada Soli Jibia, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, su ma suka yi irin wannan goyon baya.
“Yau muna tsaye a gabanku cike da alfahari da haɗin kai. Ina alfaharin sanar da ku cewa mambobi 34 na majalisar dokokin jihar Katsina, bayan dogon nazari da tattaunawa, sun yanke shawara ɗaya bisa haɗin kai domin marawa Gwamna Dikko Umaru Radda baya a takararsa ta karo na biyu."
- Nasiru Yahaya
Meyasa ƴan majalisa suka goyi bayan Dikko Radda
Ya bayyana cewa shawarar da suka yanke ta samo asali ne daga bincike da suka yi kan ayyukan gwamnan da kuma goyon bayan da suka samu daga jama’ar da suke wakilta daga faɗin jihar.
Nasiru Yahaya wanda ya yaba da salon jagorancin Gwamna Radda na haɗin kai, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara a fannonin yaƙi da rashin tsaro, gyaran harkar ilimi, bunƙasa noma, ci gaban masana’antu da sauransu.
Ya ce waɗannan ƙoƙarin da gwamnan ya yi sun sa jihar ta shiga turbar cigaba mai ɗorewa da wadata.
Ƴan majalisar sun kuma ɗauki alƙawarin goyon baya, biyayya ga tazarcen Gwamna Radda, inda suka yi kira ga dukkan ƴaƴa maza da mata na jihar su haɗu wajen tallafawa wannan yunƙuri na ci gaba da ɗorewa.

Source: Facebook
Za a siyawa Radda fom a 2027
Haka kuma sun yanke shawarar sayen fom ɗin takararsa a shekarar 2027 a matsayin hujja ta cikakken goyon bayansu.
“Bugu da ƙari, mun yanke shawarar cewa za mu saya masa fom ɗin neman takara a 2027 domin nuna cikakken goyon bayamu.”
“Wannan hukuncin ba a ɗauke shi da wasa ba. Sakamakon bincike ne mai zurfi, ra’ayoyin jama’a daga ƙasa, da kuma imaninmu da shugabancin Gwamna Radda."
- Nasiru Yahaya
Ra'ayinsu ne wannan
Sahabi Abdulrahman ya shaidawa Legit Hausa cewa matsayar da ƴan majalisar suka cimmawa ra'ayinsu ne kawai ba na mutanen jihar Katsina ba.
"Sam yanzu ba lokacin yin hakan ba ne, yadda ake fama da matsalar rashin tsaro bai kamata a ɗauko batun zaɓen 2027 tun yanzu ba."
"Kamata ya yi su maida hankali wajen yin aiki tare da gwamnati don ganin an shawo kan matsalar rashin tsaro."
- Sahabi Abdulrahman
Gwamna Radda ya sha alwashi kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Gwamna Radda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa wajen ɗaukar matakan kawo ƙarshen matsalar.
Dikko Radda ya yi waɗannan kalaman ne bayan yaje wata ziyarar jaje sakamakon wani hari da ƴan bindiga suka kai.
Asali: Legit.ng


