Majalisa za Ta Yi Amfani da Dattawan Najeriya domin Yi wa Fubara da Wike Sulhu

Majalisa za Ta Yi Amfani da Dattawan Najeriya domin Yi wa Fubara da Wike Sulhu

  • Majalisar Tarayya ta sanar da shirin kafa kwamiti na musamman domin sasanta rikicin siyasa da ya yi kara kamari a jihar Ribas
  • Abbas Tajudeen ya ce kwamitin zai hada da manyan dattawan kasa domin dawo da zaman lafiya da tsarin dimokuradiyya a jihar
  • Rikici tsakanin Gwamna Simi Fubara da tsohon uban gidansa, Nyesom Wike, ya jawo tashin hankali da ya kai ga ayyana dokar-ta-baci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya bayyana cewa za a kafa kwamiti na musamman domin sasanta rikicin siyasa da ya dabaibaye jihar Ribas.

Abbas Tajudeen ya bayyana hakan ne a zaman majalisa bayan hutun bukukuwan Sallah da Easter, ya ce za a hada gwiwa da Majalisar Dattawa wajen kafa kwamitin.

Kara karanta wannan

Abuja: Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan 1.78 ga majalisa

Majalisa
Majalisa za ta kafa kwamitin sulhu kan rikicin Rivers. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa ya ce kwamitin zai kunshi sanannun dattawan kasa wadanda za su jagoranci tattaunawa, sulhu da dawo da tsarin dimokuradiyya a jihar.

Kwamitin majalisa kan rikicin Rivers

Tun bayan da Majalisar Wakilai ta amince da dokar-ta-bacin da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a Ribas, ta kafa kwamitin wucin gadi mai mambobi 21.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamitin ya kasance karkashin jagorancin, Farfesa Julius Ihonvbere.

Kwamitin ya fara tuntubar manyan masu ruwa da tsaki domin duba hanyoyin tabbatar da doka da oda a jihar Ribas.

Shugaban majalisar ya ce sabon matakin na kafa kwamitin sulhu na daga cikin kokarin majalisar wajen wanzar da zaman lafiya da kuma sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya daura mata.

Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin sa-ido

A bangare guda, Majalisar Dattawa ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sa ido kan ayyukan Ibok-Ete Ibas da Shugaba Tinubu ya nada a matsayin shugaban rikon kwarya a jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gano yadda gwamnatocin Najeriya ke jawo talauci a kasa

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa an kafa wannan kwamiti ne domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gwamnati a lokacin rikon kwarya.

Punch ta wallafa cewa Akpabio ya ce za a iya sake duba tsarin kwamitin idan bukatar hakan ta taso bayan tattaunawa da sauran bangarori.

Majalisa
Majalisar dattawa ta kafa kwamitin lura da rikicin Rivers. Hoto: Nigerian Senate
Source: UGC

Ana sa ran zaman lafiya zai dawo Ribas

Yanzu haka an zuba ido kan ganin rawar da kwamitin sulhu da na sa ido za su taka wajen dakile rikicin siyasar da ke barazana ga zaman lafiya da dimokuradiyya a Ribas.

Ana fatan cewa matakan da majalisa ke dauka za su haifar da da mai ido, musamman idan aka tabbatar da adalci da gaskiya wajen tafiyar da sulhun.

Majalisa ta yi magana kan kisan Edo

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta yi magana kan Hausawa 16 da aka kashe a jihar Edo suna dawowa Kano hutun sallar azumin 2025.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila daga jihar Kano ne ya gabatar da kudiri game da mutanen da aka kashen a zaman majalisar.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya goyi bayan kudirin da Kawu Sumaila ya gabatar, ya ce yana da muhimmanci a tabbatar da adalci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng