Kurunkus: Atiku Abubakar Ya Bayyana Matsayarsa kan Yiwuwar Ficewa daga PDP kafin 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya musanta rahoton da ke cewa yana shirin fita daga PDP zuwa APC
- Atiku ya ce ba zai bar PDP kuma zai jagoranci haɗakar ƴan adawa da za ta fatattaki APC daga fadar shugaban kasa a 2027
- Wazirin Adamawa ya yi wannan furucin ne da ya karɓi bakuncin tawagar mata ƴan majalisar amintattun jam'iyyar PDP (BoT)
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Dan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya karyata jita-jitar da ke cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyarsa zuwa APC mai mulki.
Wazirin Adamawa ya jaddada cewa yana nan daram a PDP kuma haɗakar da yake jagoranta za ta kawar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan furucin ne da ya karɓi baƙuncin mata ‘yan majalisar amintattu ta PDP (BoT).

Kara karanta wannan
APC ta nakasa shirin Atiku, ƴan takarar gwamna 2 da mambobi 12,000 sun bar PDP da ACP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar mata ƴan majalisar BoT sun kai masa ziyara ne domin neman mafita daga tabarbarewar jam’iyyar da rokon Atiku ya ceto PDP daga rugujewa.
Matan sun je wurin Atiku ne ƙarƙashin jagorancin tsohuwar ministar harkokin mata kuma tsohuwar shugabar matan PDP, Hajia Inna Ciroma.
Atiku Abubakar ya dage kan batun haɗaka a 2027
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya jaddada bukatar ƙulla ƙawance a tsakanin ƴan adawa domin fatattakar gwamnatin APC a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana cewa wannan yunƙuri na ƙulla kawance ba wai dabarar siyasa ba ce kawai, sai dai abu ne da ya zama tilas domin fatattakar APC da sake gina Najeriya.
Jagoran ƴan adawan Najeriyan ya shaida wa tawagar matan cewa haɗakar za ta yi aiki kuma za a samu sakamako mai kyau.
Atiku ya tuna yadda aka yi a Jamhuriya ta biyu
Ya bayyana cewa a zamanin Jamhuriyya ta Biyu, jam’iyyar NPN ta ƙulla yarjejeniya da NPP, suka kira shi da ƙawancen da NPN-NPP.
Atiku ya ƙara cewa idan an cimma wannan haɗaka da yake jagoranta, martaba da ƙimar jam’iyyar PDP ba za ta samu wata illa ba.

Source: Twitter
Har ila yau, ya sanar da su cewa yana jagorantar haɗakar ne tare da manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, domin gina sabuwar Najeriya da ‘yan ƙasa ke mafarkin samu.
Ya ce wannan yunƙuri yana samun goyon baya daga al’ummar da ke da sha’awar kwato ƙasarsu daga kangin da take ciki a yanzu, rahoton Daily Trust.
Atiku ya soki matsayar gwamnonin PDP
A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya saɓawa gwamnonin PDP kan hanyar da ya kamata a bi wajen kayar da Shugaba Tinubu a 2027.
Atiku ya soki matsayar gwamnoni 11 na PDP da suka nesanta jam’iyyar daga hadin gwiwar da tsohon mataimakin shugaban kasar ke jagoranta.
Ya jaddada cewa babu wata hanya da za a kawo ƙarshen mulkin APC a Najeriya matuƙar ƴan adawa ba su hakura sun haɗa kansu wuri guda ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
