‘Dalilin da Ya Sa Tinubu Ka Iya Fuskantar Cikas a Takararsa na Zaben 2027’

‘Dalilin da Ya Sa Tinubu Ka Iya Fuskantar Cikas a Takararsa na Zaben 2027’

  • Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya ce Tinubu na iya fuskantar matsaloli da za su hana shi tsayawa takara a 2027
  • Eze ya soki gwamnatin Tinubu da rashin tabuka abin a zo a gani, yana mai cewa yunwa da kashe-kashe sun yi yawa
  • Ya ce mutane na tambayarsa makomar tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, yana mai cewa ya cancanci shugabanci don ceto Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya yi karin haske kan neman takarar Shugaba Bola Tinubu.

Eze ya bayyana cewa Bola Tinubu na iya fuskantar cikas wajen tsayawa takara a zaben shekarar 2027 duba da rahoton da ke hannun Amurka.

Jigon APC ya yi magana kan takarar Tinubu
Jigon APC ya ce watakila Tinubu ya fuskanci matsala a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Jigon APC ya magantu kan takarar Tinubu

Eze, wanda ya kasance aminin tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Post.

Kara karanta wannan

2027: Buba Galadima ya hada Tinubu, Atiku da El Rufa'i, ya gyara musu zama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce akwai yiwuwar zaben shekarar 2027 ya zo da abubuwa masu daukar hankali da kuma ba da mamaki.

A cewarsa, akwai wani rahoto da ake zargin gwamnatin Amurka na da shi game da Bola Tinubu, kuma idan aka saki shi, zai iya shafar makomar siyasar shugaban kasar.

Ya ce:

“2027 za ta cika da mamaki, Tinubu na iya rasa damar tsayawa takarar da yake kokarin murdewa domin samun nasara."

'Dalilai da za su hana Tinubu takara' - Eze

Eze ya kara da cewa faduwar wannan gwamnati da muke gani a fili ya isa ya hana Tinubu tunanin sake tsayawa takara.

Eze ya yi Allah-wadai da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa ta gaza wajen shawo kan matsalolin da ke addabar kasar kamar yunwa, tabarbarewar tattalin arziki, da rashin tsaro.

“Gwamnati da ke mayar da hankali wajen murde tsarin zabe domin ci gaba da mulki a 2027 ta gaza, yunwa, rashin tsaro, da kashe-kashe sun mamaye kasar."

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi bangaren da Buhari zai yi wa APC amfani a zaɓen 2027

- Cewar Eze

Eze ya yi magana kan Rotimi Amaechi

Eze ya bayyana cewa wannan ba irin mulki ba ne da ya dace da tsarin dimokradiyya, cewar rahoton Tribune.

Ya ce jama’a na kiransa kullum suna tambayar makomar siyasar Amaechi da ko zai fito takara.

Har ila yau, Eze ya bayyana Amaechi a matsayin dan kasa mai kishin kasa wanda zai iya sadaukar da komai domin ganin Najeriya ta ci gaba.

Ya kara da cewa:

“Jama’a na tambayata kullum kan Amaechi, shi ne zai iya sadaukar da komai domin ceto Najeriya."

Ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugabanni irin Amaechi domin dawo da martabar kasar.

Bwala ya shawarci Atiku kan zaben 2027

Kun ji cewa hadimin Bola Tinubu ya shawarci Atiku Abubakar ya hakura da neman mulki saboda alamu sun nuna ba zai shugabanci Najeriya ba.

Daniel Bwala ya ce Allah ke ba da mulki ga wanda ya so amma ga dukkan alamu Allah ba zai ba Atiku damar shugabancin kasar nan ba.

Bwala ya buƙaci Atiku ya haɗa kai da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin cika burinsa na inganta Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.