Siyasa Rigar 'Yanci: 'Yan Majalisar Wakilai 8 Sun Sauya Sheka zuwa APC, PDP
- Guguwar sauya sheƙa ta leƙa majalisar wakilan Najeriya a ranar Talata, 6 ga watan Mayun 2025
- Wasu ƴan majalisar wakilai guda shida sun watsawa PDP ƙasa a ido bayan da suka koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya
- Ƴan majalisar sun bayyana cewa sun sauya sheƙar ne saboda rikicin cikin gida da rabuwar kawunan da ake samu a jam'iyyar da suke ciki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƴan majalisar wakilai shida sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Hakazalika wasu ƴan majalisar wakilai guda biyu daga jam’iyyar LP sun koma PDP.

Source: Twitter
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya sheƙarsu yayin zaman majalisar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan majalisar da suka koma PDP
Obetta Chidi, mai wakiltar mazaɓar Nsukka/Igbo-Eze ta Kudu a jihar Enugu, ya sauya shea daga jam'iyyar LP zuwa PDP.

Kara karanta wannan
"Guguwar Tinubu": Kakakin majalisar dokoki da ƴan majalisa 21 sun fice daga PDP zuwa APC
Dennis Agbo, wanda ke wakiltar mutanen mazaɓar Igbo-Eze ta arewa/Udenu a jihar Enugu, shi ma ya bar LP zuwa PDP.
Ƴan majalisar da suka koma APC
Victor Nwokolo, wanda ke wakiltar mazaɓar Ika ta Arewa maso gabas/Ika ta Kudu a jihar Delta, ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Julius Pondi, mai wakiltar mazaɓar Burutu a jihar Delta shi ma ya bar PDP zuwa APC.
Thomas Ereyitomi, wanda ke wakiltar mazabar Warri ta Arewa/ta kmKudu/ta Yamma a jihar Delta ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Nicholas Mutu, dan jam’iyyar PDP wanda ke wakiltar Bomadi/Patani a jihar Delta, ya koma jam’iyyar APC. Nicholas Mutu ya kasance a majalisar wakilai tun daga 1999.
Ukodhiko Jonathan, wanda ke wakiltar mazabar Isoko ta Arewa/ta Kudu a jihar Delta, ya fice daga PDP zuwa APC.
Ezechi Nnamdi, sabon ɗan majalisa da ke wakiltar Ndokwa/Ukwuani a jihar Delta, ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.

Source: Facebook
Meyasa ƴan majalisar suka sauya sheƙa?
Ƴan majalisun sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da rabuwar kawuna da suka dabaibaye jam’iyyunsu ne suka tilasta musu sauya sheƙa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan
APC ta nakasa shirin Atiku, ƴan takarar gwamna 2 da mambobi 12,000 sun bar PDP da ACP
Sun ce irin waɗannan rikice-rikice na hana su cika alkawuran da suka ɗauƙa lokacin kamfe, kuma suna da cikakken goyon bayan mutanen mazaɓunsu wajen yanke shawarar ficewa daga jam'iyyunsu.
Sauya sheka ta zama ruwan dare
Tsalle daga jam'iyya zuwa wata jam'iyyar wani hali ne da 'yan siyasar Najeriya, amma yadda abubuwa ke canzawa a wannan zamani ya nuna cewa siyasar kasar na fuskantar wani sabon salo.
A da, sauya sheƙa yawanci na faruwa ne kafin ko bayan babban zaɓe, amma a yanzu yana zama tamkar wata hanya ta daidaita muradun siyasa da kare matsayin mutum a cikin yanayin rikice-rikicen jam’iyya.
'Yan siyasa na ganin canjin jam’iyya a matsayin wata hanya ta tsira daga ruɗanin da ke faruwa a cikin gida, musamman idan babu daidaito a shugabanci ko kuma idan sun ji suna rasa tasiri a matsayinsu na wakilai.
Sau da yawa, waɗanda ke ficewa daga jam’iyya suna danganta hakan da “gocewar amana” daga shugabanninsu ko rashin iya cika alkawuran da suka ɗauka ga jama’a.
Wannan yana nuna cewa sauya sheƙa ba kawai game da kujerar siyasa ba ne — yana da nasaba da tabbatar da muradin siyasa da cigaba.
Haka kuma, abubuwan da ke faruwa sun nuna cewa jam’iyyun siyasa ba su da cikakken tsarin da ke daure mambobi a tsari na dogon lokaci.
Rashin dimokuraɗiyya a cikin gida, keta tsarin raba madafun iko, da tsoma baki cikin duk wani yunkuri na shugabanci na daga cikin dalilan da ke sa ‘yan siyasa jin cewa dole ne su nemi wata mafita a waje.
Ƴan majalisar dokoki sun koma APC a Delta
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan majalisar dokokin jihar Delta mai arziƙin mai sun sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Daga cikin masu sauya sheƙar akwai kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Rt. Hon Emomotimi Guwor, tare da ƴan majalisa 21, waɗanda suka sanar da sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a hukumance.
Ƴan majalisar sun bayyana cewa sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki a Najeriya ne saboda rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP a yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Asali: Legit.ng
