Ana Shirin Hadaka, Peter Obi Ya Gamu da Matsala a Jam'iyyar LP

Ana Shirin Hadaka, Peter Obi Ya Gamu da Matsala a Jam'iyyar LP

  • Jam'iyyar LP mai adawa a jihar Anambra ta gamu da koma baya bayan ɗaya daga cikin jiga-jiganta ya sanar da yin murabus
  • Oseloka Obaze wanda makusancin Peter Obi ne ya sanar da murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam'iyyar
  • A cikin wasiƙar ya yi bayani kan dalilan da suka sanya ya yanke shawarar barin jam'iyyar wacce ya koma cikinta a shekarar 2022

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Oseloka Obaze makusancin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi murabus daga jam'iyyar.

Oseloka Obaze ya bayyana murabus ɗinsa ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam’iyyar LP na mazaɓar Ochuche, a ƙaramar hukumar Ogbaru ta jihar Anambra.

Oseloka Obaze ya yi murabus daga LP
Makusancin Peter Obi ya fice daga jam'iyyar LP Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Oseloka Obaze, wanda tsohon jami’in diflomasiyyar majalisar ɗinkin duniya ne, ya taɓa rike muƙamin sakataren gwamnatin jihar Anambra a lokacin mulkin Peter Obi, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Hadakar Atiku ta fara gigita APC, an fallasa abin da Tinubu ke kullawa 'yan adawa

Ya yi aiki tare da Peter Obi a matsayin mai ba da shawara ta fuskar siyasa da kuma jagoran jam’iyyar har zuwa lokacin da ya yi murabus.

Makusancin Peter Obi ya bar jam'iyyar LP

Obaze ya bayyana cewa dalilin barinsa jam’iyyar LP shi ne don nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aka gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna da jam’iyyar ta gudanar a ranar 5 ga watan Afrilu, 2025 a jihar Anambra.

“A cikin wannan wasiƙa, ina sanar da murabus ɗina daga jam’iyyar LP."
"Hanyoyin tsarawa, yadda aka gudanar, da sakamakon zaɓen fidda gwanin jam’iyyar LP da aka yi a ranar 5 ga watan Afrilu, 2025 a Awka, sun cika da kura-kurai, da ke nuna alamun rashin gaskiya."
“Ba su yi daidai da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ba, kuma sun saɓawa ƙimar da jam’iyyar ke iƙirarin tsayawa kai da kai da kuma ainihin ƙa’idojin dimokuraɗiyya. Saboda haka, daga yau, na daina kasancewa cikin LP".

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan bindiga kwanton bauna, an samu nasara kan miyagu

- Oseloka Obaze

Hakazalika a kuma ambato rikicin shugabanci da ke faruwa a matakin ƙasa a jam’iyyar LP da kuma gazawar jam’iyyar wajen warware rikicin tsakanin Julius Abure, shugaban tsagin jam’iyyar, da Nenadi Usman, shugabar kwamitin riƙo.

Oseloka Obaze ya fice daga LP
Maskusan Peter Obi ya yi murabus daga jam'iyyar LP Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wace jam'iyya Oseloka Obaze zai koma?

Sai dai Obaze bai bayyana jam’iyyar siyasa da zai koma ba bayan murabus ɗinsa daga LP.

A baya dai, ya bar jam’iyyar PDP a shekarar 2022, mako guda kafin Peter Obi ya bar jam’iyyar ya koma LP.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake zargin jam'iyyar mai rike da gwamnatin kasa da ya yi wa 'yan adawa dauki daya-daya.

Dalilin Wike na korar Peter Obi daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi magana kan ficewar Peter Obi daga jam'iyyar.

Dele Momodu ya fito ya na zargin cewa Nyesom Wike ne ya yi sanadiyyar ficewar Peter Obi daga jam'iyyar a shekarar 2022.

Jigon na PDP ya nuna cewa Wike ya yi hakan ne domin samun tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng