Shirin 2027: Gwamnonin PDP da Wike Sun yi Zama don Dawo da Zaman Lafiya a Jam’iyyar
- Alamu sun nuna an samu sabuwar yarjejeniya tsakanin gwamnonin PDP da Wike a Legas kwanan nan
- An tattauna rikicin Ribas da matsalolin shugabancin jam’iyya da duk wasu matsalolin da ake tsammanin za su kifar da jam’iyyar
- Makinde ya ce dole ne a nemi mafita ta siyasa kafin 2027. A halin yanzu dai PDP na ci gaba da fuskantar koma-baya
Jihar Legas - Gabanin babban zaben shugaban kasa na 2027, wasu gwamnoni da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP sun gana da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike kan batun zaman lafiyar jam’iyya.
Wata majiya daga jam’iyyar ta shaidawa Sunday PUNCH cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya wakilci gwamnonin na PDP a taron da aka yi da Wike a Legas makon jiya.
A cewar majiyar, sun tattauna rikicin siyasa da ke tsakanin Wike da Gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar.

Source: Facebook
Hakazalika, sun yi batutuwa kan matsalolin shugabancin yankin Kudu masu Kudu da batun Sakatare na kasa wanda har yanzu ba a warware ba tun watan Disamban 2024.
Rikicin PDP a wannan mulkin na Tinubu
Tun bayan zaben 2023, PDP na fama da rikicin cikin gida, inda yunkurin sasanci daga NWC, BOT, NEC da inuwar gwamnonin PDP ya gaza haifar da da mai ido ba, sai ma kara jefa jam’iyyar cikin rudani da rabuwar kai.
Rikicin ya haifar da bacin ran wasu jiga-jigai a jam’iyyar, har wasu suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
A ranar 23 ga Afrilu, Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa sun sauya sheka tare da wasu 'yan jam’iyyar zuwa APC, wanda hakan ya jefa PDP cikin matsanancin hali gabanin 2027.
Bayan ganawa da Wike a Legas
Majiyar ta ce bayan ganawar a Legas, Makinde ya yi alkawarin sanar da sauran gwamnoni, yayin da Wike zai sanar da magoya bayansa sakamakon ganawar.
Wike ya nuna bacin ransa kan yadda gamayyar gwamnonin ke daukar matakai ba tare da la'akari da dokokin jam’iyyar ta PDP ba.

Kara karanta wannan
Uwar Bari: Fubara zai kara zama da Wike a shirin sulhu a Rivers, APC da PDP sun magantu
Ya kuma jaddada cewa bai da niyyar barin PDP, sai dai ya bukaci da a sake duba wasu matsalolin da suka hada da rikicin Ribas, shugabancin Kudu maso Kudu da batun Sakatare na kasa domin a samu daidaito da hadin kai.
Makinde kan halin wasu mambobin PDP
Makinde ya koka kan yadda wasu manyan mambobin jam’iyyar ke nuna rashin mutunta gwamnoni, wanda ke kara dagula lamura.
Daga karshe sun amince cewa a soke duk wasu karar siyasa da ke gaban kotu sannan a nemi mafita ta siyasa.
Wani babban jigo daga kwamitin NWC ya tabbatar da aukuwar ganawar inda ya bayyana cewa tana da nufin dawo da hadin kai a jam’iyyar.
Yadda taro ya gudana
Shima Timothy Osadolor, mataimakin shugaban matasa na PDP, ya bayyana cewa jam’iyyar za ta dawo da karfinta.
Ya ce:
“Wannan jam’iyya ce ta kowa da kowa. APC tamkar jirgi ne da ke cike da kaya; lokaci na nan da ba da jimawa ba za ta nutse.”
Atiku na jawo rikici a jam’iyyar, Jiga-jigan PDP
A bangare guda, wasu jiga-jigan jam’iyyar sun zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da haddasa rikicin da PDP ke ciki.
Sun koka cewa, ya kamata fadi a fili cewa ba zai tsaya takara a 2027 ba. Sun bayyana cewa a baya Atiku ya fice daga PDP da wasu gwamnoni amma jam’iyyar ta tsira, don haka za su ci gaba da adawa da shi.
Asali: Legit.ng
