Haɗama: APC Ta Cire Sunan Ɗan Takararta kan Zargin Karbar Albashi Har Guda 2
- Jam’iyyar APC ta cire Samad Ogunbo daga takarar shugabancin karamar hukumar Eti-Osa ta Gabas saboda karɓar albashi sau biyu daga gwamnati lokaci guda
- Takardu sun nuna Ogunbo yana karɓar albashi daga hukumar SUBEB da kuma matsayin mai sanya ido da harkar lafiya a karamar hukuma tun 2022
- Hukumar SUBEB ta ce ba ta san Ogunbo yana da wani mukami a karamar hukuma ba, kuma hakan ya saba dokokin aikin gwamnati a Jihar Lagos
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - An zargi Samad Ogunbo da samun albashi daga wurare biyu na gwamnati lokaci guda.
Ogunbo yana daga cikin masu neman takarar shugabancin karamar hukuma a jihar Lagos a karkashin jam'iyyar APC.

Source: Twitter
APC ta cire dan sunan dan takara a Lagos
Sahara Reporters ta ce an samu Ogunbo yana aiki a hukumar SUBEB da kuma matsayin mai sanya ido a wata karamar hukuma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan samun korafi game da wannan matsayi biyu a lokaci guda, jam’iyyar APC ta cire Ogunbo daga takarar shugabancin karamar hukumar Eti-Osa ta Gabas.
Majiyoyi sun ce an cire Ogunbo ne saboda korafin da ke da nasaba da samun albashi har kashi hbiyu.
A baya, Ogunbo na fuskantar zargin yaudarar gwamnati da karya dokar aikin gwamnati a Jihar Lagos.
An tabbatar da cewa Ogunbo yana aiki da SUBEB da kuma matsayin mai sanya ido a bangaren lafiya a karamar hukuma tun Afrilu 2022.

Source: Facebook
Hukumar SUBEB ta magantu kan lamarin
Wata wasika daga SUBEB ta tabbatar da cewa Ogunbo yana cikin ma'aikatan hukumar duk da yana samun albashi daga karamar hukuma.
SUBEB ta bayyana mamaki ganin cewa Ogunbo da wani mutum na karɓar albashi daga SUBEB da karamar hukuma lokaci guda.
Lokacin da aka tambayi SUBEB kan matsayin aikin Ogunbo, hukumar ta tabbatar da cewa yana cikin ma’aikatanta.
Hukumar ta ce ba ta da masaniyar cewa Ogunbo yana samun albashi daga karamar hukuma tare da rike mukamin siyasa.
Ta ce:
"Saboda wasikar ku ta 4 ga Afrilu, 2025, da lamba EOELCDA/CH/01/VOL.1/099, game da matsayin aiki da albashin Samad Ogunbo da Rasak Abidemi.
"Ina so in fayyace cewa a cewar bayanan da ke gabana, mutanen biyu na aiki a hukumar ilimi ta Eti-Osa.
"Har ila yau, ofishinmu ya yi mamakin jin cewa suna cikin jerin albashi na hukumar ku ba tare da sanarwar mukamin siyasa ba.
"Za mu taimaka da bincikenku idan bukatar hakan ta taso. Muna mika gaisuwa da godiya."
Kungiyar Yarbawa ta goyi bayan Tinubu
A wani labarin, Kungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana goyon bayanta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin kammala shekaru takwas a mulki.
A cewar Afenifere, wasu na amfani da kalmar "Gwamnatin Yarbawa" don hana Tinubu wa’adi na biyu, wanda suka ce ba gaskiya ba ne.
Afenifere ta ce kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi shekaru takwas ba tare da cikas ba, dole ne a bar Tinubu ya kammala duka wa'adinsa.
Asali: Legit.ng

