Ana Kukan ba Kudi, PDP Za Ta Karbi Naira miliyan 8.5 daga Masu Son Takarar Ciyaman

Ana Kukan ba Kudi, PDP Za Ta Karbi Naira miliyan 8.5 daga Masu Son Takarar Ciyaman

  • Jam’iyyar PDP reshen birnin tarayya ta fara sayar da fom ɗin takarar ciyaman da kansiloli, inda fom din ciyaman ya kai Naira miliyan 8.5
  • Yayin da masu sha'awar takarar kujerar kansila za su biya Naira miliyan 1.5, a hannu daya, jam'iyyar ta ce mata za su samu fom din a kyauta
  • PDP ta ce ita ce jam’iyya ɗaya tilo da ta tsaya tsayin daka cikin shekaru 26 na dimokuraɗiyya tare da samun sababbin mambobi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar PDP, reshen babban birnin tarayya (FCT) ta kaddamar da fara sayar da fom ɗin nuna sha’awa da na tsayawa takarar kujerar ciyaman da kansiloli.

Rahoto ya nuna cewa, PDP ta shaida wa masu sha'awar tsayawa takarar shugabancin ƙaramar hukuma a Abuja, za su iya Naira miliyan 8.5 domin sayen fom.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban APC ya rikita mata lissafi bayan yin murabus, ya soki salon Ganduje

Jam'iyyar PDP ta fara sayar da fom din takarar ciyaman da kansila a Abuja.
Manyan jagororin PDP a wani taro da suka gudanar a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Zaben ciyaman: PDP ta fara sayar da fom a Abuja

Hakazalika, jam'iyyar ta ce wadanda ke sha'awar tsayawa takarar kujerar kansila kuwa, za su biya Naira miliyan 1.5 domin samun fom ɗin, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakatariyar yaɗa labaran PDP a FCT, Josephine C. Itoyah, ta bayyana hakan a yayin ƙaddamar da fara sayar da fom ɗin takarar ciyaman da na kansiloli a hedkwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Talata.

Taron ya samu halartar mai duba lissafin kudi na jam’iyyar, reshen birnin tarayya Abuja, Joshua Yohana da sakataren jam’iyyar, Rabo Lucky Iyah.

PDP za ta ba mata fom din takara kyauta

Josephine ta ƙara da cewa za a bai wa mata da ke sha'awar tsayawa takara fom ɗin shugaban karamar hukuma da na kansiloli kyauta ba tare da biyan ko sisi ba.

Jam’iyyar za ta kuma rage kudin fom ga masu buƙata ta musamman (PWDs) domin samar da damar shigarsu cikin harkokin siyasa.

Kara karanta wannan

"Sai yanzu ka san yana da kima?" El Rufa'i ya tunawa Ganduje ya kira Buhari Habu na Habu

Ta ce PDP ita ce jam’iyya ɗaya tilo da yi saura, kuma har yanzu take da tasiri a cikin shekaru 26 na mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Farashin fom din PDP a zaben 2021

A shekara ta 2021, PDP ta kayyade kudin fom ɗin takarar shugabanci a Abuja a kan N400,000, yayin da na nuna sha’awa ya kasance N100,000.

Masu neman kujerar kansila kuwa sun biya N75,000 don fom ɗin takara, sannan N25,000 don fom ɗin nuna sha’awa, inji rahoton ThisDay.

Jam’iyyar ta kuma sa N3,000 a matsayin kudin fom ɗin wakilai na wucin-gadi daga mazabu (three-man ward delegates) da kuma wakilan ƙasa (national delegates).

PDP ta shawarci dukkan masu sha’awar takara da wakilan da aka zaɓa da su tafi ofishin Sakataren Kuɗi na Ƙasa don biyan kudin fom.

Wike ya kwace filin hedikwatar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kwace filin da jam’iyyar PDP ke amfani da shi a matsayin hedkwata, kan zargin kin biyan haraji na tsawon shekaru 20.

Kara karanta wannan

Ganduje ya ce Kwankwaso zai bar NNPP, ya dawo jam'iyyar APC

Hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) ta bayyana cewa PDP ta gaza biyan harajin filin daga watan Janairun 2006 zuwa Janairun 2025, duk da sanarwar da gwamnati ta yi.

Kwace filin ya yi daidai da tanadin sashe na 28(5) na dokar mallakar filaye, wanda ya bai wa gwamnati damar kwace filin da ba a biya haraji ko cika sharuddan mallaka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com