"Na Cancanci Zama Shugaban Ƙasa," Gwamna Ya Yi Bayanin Shirinsa a Zaɓen 2027
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana cewa ya na da cancantar rike kujera lamba ɗaya a Najeriya watau Mai girma shugaban kasa
- Makinde, wanda ke wa'adin mulki na biyu a matsayin gwamna ya ce idan ya yanke shawarar neman kujerar shugaban ƙasa, zai fito ya yi bayani
- Gwamnan ya jaddada cewa yanzu ya maida hankali wajen sauke nauyin da al'ummar Oyo suka ɗora masa, kuma ba zai bari a ɗauke masa hankali ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana da cikakkiyar ƙwarewa da gogewar zama shugaban ƙasa a Najeriya.
Gwamna Makinde ya yi ikirarin cewa yana da duk abin da ake buƙata na cancantar riƙe muƙami lamba ɗaya a ƙasar nan.

Asali: Facebook
Makinde, wanda ke wa’adin mulki na biyu a matsayin gwamna kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan PDP, ya faɗi hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels tv a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Menene shirin Gwamna Makinde a 2027?
Ya ce zaben 2027 ba zai kasance tsakanin APC da PDP ba, illa tsakanin ‘yan Najeriya da jam’iyya mai mulki wato APC.
“Ina da tabbacin cewa ina da kwarewa da cancantar rike mafi girman ofishin siyasa a kasar nan.
"Amma tambaya ita ce, shin wannan shi ne abin da ‘yan Najeriya ke bukata a yanzu? Shin jam’iyyata za ta ce hakan ne ya dace? Ba mu da amsar hakan tukuna.”
- In ji Makinde.
Ya ce har yanzu lokacin bayyana aniyyarsa ta neman takarar shugaban ƙasa bai yi ba, saboda a cewarsa akwai bukatar gyara jam’iyyar PDP ta dawo kan turba.
“Idan tafiyar siyasata ta tsaya a nan kaɗai, ba wata matsala zan yi farin ciki da hakan. Babu wanda zai tsara mani ajenda, ni zan tsara komai da kaina,” inji Makinde.

Asali: Facebook
Shin Makinde ya shirya gwabza wa da Tinubu?
A lokacin da aka tambaye shi ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027, ya ce ba zai yanke hukunci a gaggauce ba kuma ba zai yi siyasar da ba ta da tushe ba.
“Na mayar da hankali ne kan aikin da al’ummar Oyo suka dora mani. Ba zan shiga siyasar da ba ta da amfani ba. Idan lokaci ya yi, kuma na yanke shawara, zan fito fili na yi cikakken bayani.”
Makinde ya kuma jaddada cewa yana da kyakkyawan tarihi wajen cika alkawari da kuma tsaya wa al’umma, inda ya ce zai ci gaba da mayar da hankali kan ci gaban jama’arsa.
Makinde zai zaɓi magajinsa a Oyo
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya bayyana shirinsa na zaƙulo wanda zai gaji kujerarsa a zaɓen 2027 a jihar Oyo.
Makinde ya tabbatarwa al'ummar jihar Oyo cewa zai sanar da sunan wanda yake so su zaɓa ya zama magajinsa a watan Janairu, 2026.
Gwamnan ya gode wa shugabannin da malaman addinin musulunci bisa goyon bayan da suke ba gwamnatinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng