"Ya Hango Kuraye a Hadakar Jam'iyyu," APC ba Ta Maraba da Kwankwaso a Kano
- APC ta Kano ta bayyana damuwa kan zargin yunkurin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na komawa cikinta a cikin kwanaki masu zuwa
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyar NNPP ta mutu, kuma sun samu labarin cewa Kwankwaso zai dawo APC
- Duk da Ganduje ya ce suna maraba da Kwankwaso, APC a Kano ta bayyana cewa dawowar jagoran NNPP cikin jam’iyyar babbar matsala ce
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –APC ta Kano ta bayyana cewa maganganun jagora a NNPP, Buba Galadima, da rubuce-rubucen da magoya bayan jam’iyyar ke yi ba zasu sa su karɓi Rabi’u Musa Kwankwaso hannu bibbiyu ba.
Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar APC, Ahmed S. Aruwa, ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da Legit, ganin yadda maganganu ke ƙara ƙarfi a kan sauya shekar Sanata Kwankwaso.

Kara karanta wannan
"Sai yanzu ka san yana da kima?" El Rufa'i ya tunawa Ganduje ya kira Buhari Habu na Habu

Asali: Facebook
A yammacin Talata, Punch ta ruwaito cewa da kansa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da cewa Kwankwaso na hanyarsa ta komawa tsohuwar jam’iyyar da ya bari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya sa APC ba ta son Rabiu Kwankwaso
'Kwankwaso ba ya biyayya’ — Aruwa
Daily Post ta wallafa cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje zai iya dawowa cikinta, kuma suna maraba da shi.
Amma APC ta Kano na ganin cewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba ya bin na gaba da shi; sai dai shi a bi shi. Aruwa ya ce hakan na iya kawo tarnaki ga tafiyarsu a jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
Ya bayyana cewa tun da suka ji Buba Galadima yana yabon shugaban ƙasa, har ma da cewa ya samu wa diyarsa aikin yi, sai aka gano lauje cikin naɗi wajen jagoran NNPP.
Ya ce:
“Ko ma menene, ko ma wane irin yanayi ne, ba ma yi masu barka da zuwa. Kuma muna gaya wa shugaban ƙasa cewa ya ɗebi abin nan da ake kira — ko dai cinnaku a zuba a cikin wandunansu — domin tun farko, shi (Kwankwaso) da mutane daban-daban ba su gama lafiya da juna ba.”
APC ta zargi Kwankwaso da tursasawa jama'a
Ahmed S. Aruwa ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, yana da halin tursasa ra’ayinsa a kan duk waɗanda yake mu’amala da su.
Ya ce:
“Haka suka yi da Malam Ibrahim Shekarau a PDP. Ya zo, ya kwace jam’iyyar, ya yi abin da ya ga dama. To, yanzu kuma Ganduje ya karɓi APC, ya zama gwamna, yanzu kuma shugaban jam’iyya ne.
"Yanzu kuma Kwankwaso ya sake lallabowa tun da kotu ta haramta masa NNPP, kuma waccan hadakar, kuraye ne cikinta — su Atiku da suka kore shi daga PDP."
“To yanzu yana ganin hanyar da ta fi masa sauƙi ita ce APC. Amma mu muna nan — wannan kare ba gudu ba ja da baya.”
An zargi Kwankwaso da cin mutuncin Tinubu
Ahmed S. Aruwa ya bayyana cewa a baya babu irin kalaman cin mutunci da Rabi’u Musa Kwankwaso bai yi wa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ba.
Aruwa ya ce:
“Ya ce Tinubu ba shi da lafiya, Tinubu ba ya iya tsayuwa, Tinubu tangadi yake yi. Ya ce zaben APC haramun ne. Shi ba zai ba da shawara a zabi APC ba. Yanzu kuma ya lallabo ya zo ya bata mana tsarin. Mu mun ce wannan abin da yake faɗa, uban kuturu ya yi kaɗan.”
Tsofaffin yan Kwankwasiyya za su koma APC
A baya, mun wallafa cewa Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da wasu fitattun ‘yan majalisar dokoki daga jam’iyyar NNPP a jihar Kano.
An gana da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, mai wakiltar Rano/Kibiya/Bunkure a majalisar wakilai.
Sauran sun hada da Hon. Aliyu Sani Madaki, dan majalisar Dala da Hon. Badamasi Ayuba, tsohon ɗan majalisar wakilai a wani yunkuri na sauya sheka daga NNPP zuwa APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng